• This is Slide 1 Title

    This is slide 1 description. Go to Edit HTML and replace these sentences with your own words.

  • This is Slide 2 Title

    This is slide 2 description. Go to Edit HTML and replace these sentences with your own words.

  • This is Slide 3 Title

    This is slide 3 description. Go to Edit HTML and replace these sentences with your own words.

Saturday, July 13, 2019

GYARAKAYANKA

Dayawan Mutane basa yada sallama,musamman wanda Allah yayima falala ta dukiya,ilimi ko matsayi hardama wasu talakawan.Duk duniya babu mai matsayin Annabi S.A.W amma duk dahaka har yara qanana yanayima sallama.Anas dan malik R.A yawuce tawajen yara,sai yayi musu sallama,sai yace:manzon Allah S.A.W yakasance yana aikata haka.(BKH&MUS)
  SANNAN MULURA DAKYAU, DUK WANDAKE YIMAKA SALLAMA IDAN YA SAMEKA AWANI GURI ZAKAJI KANA SONSHI.KAMAR YADDA YAZO A HADISAN ANNABI S.A.W YACE:BAZAKU SHIGA ALJANNAH BA HAR SAI KUNYI IMANI,BAZAKUYI IMANIBA HAR SAI KUNSO JUNA,BANA SANAR DAKU WANI ABUBA WANDA IDAN KUNA AIKATASHI ZAKUSO JUNA?SAI YACE KU YADA SALLAMA ATSAKANINKU
  ANTABAYI MANZON ALLAH,IDAN  MUTANE SUKA HADU WANENE ZAI FARA YIMA WANI SALLAMA?SAI YACE:WANDA YAFI MATSAYI AWAJEN ALLAH.(Tirmizi)
Kenan duk wanda yake fara yi maka sallama idan kun hadu,akwai yiwuwar yana da matsayi wajen Allah.Yi kokari kaima kashiga cikinsu.
 Hakanan MANZON ALLAH YACE:WANDA KE SAMAN ABUN HAWA ZAIYIMA WANDA YAKE  TAFIYA  AQAFA ASALLAMA WANDA YA KE TAFIA QASA(DAQAFA) ZAIYIMA WANDA KE ZAUNE..
 (BUKH&MUS) Allah yabamu ikon koyi da manzo s.a.w wajen yada sallama.
AMEEN.

Saturday, July 6, 2019

SUNNAH KO SUNA?

Baya daga cikin karantarwar sunnar manzon Allah S.A.W,wa'yansu dabi'u wanda dayawa yara masu tasowa ko kuma ince matasan dasuke Kiran kansu ahlussunnah sukayi fice akansu.
Kuma mafi yawa sunfi aiwatar dawannan dabi'u ga wa'yanda suke bin hanyarsu.Kadan daga cikin wa'yannan dabi'u akwai:
*Tsarkake kai,
*Jiji da kai,
*Girman kai,
*Ganin fifikon kansu akan wani
*Qasqantarda mutane
*Qin girmama nagaba dasu
*Hassada.
Shifa manzon Allah baitaba koyarda almajiransa daya daga cikin wa'yannan halayenba,baikuma taba aiwatar dasuba akan mutanensaba.
Tareda kasancewarsa Wanda yafi kowa daraja da matsayi Amma,har makiya sun tabbatarda kyawawan dabi'un manzo S.A.W,kamarsu;
-Qaskantarda kai(mutunta mutane)
-Girmamasu,
-Rashin raina mutume,
-Nuna soyayya ga mutanensa,
-Sakin fuska idan ya hadu da mutum(fara'a)
-Nuna damuwa akan damuwar wani
-Riqe sirrin mutane,
-Son alkhairi ga mutane,
-Taimaka ma mutanensa,
-Cika alkawari,
-Rikon amaana,
-Kyamar ganin anci mutuncin wani,
-Baya gorantawa idan yayi alkhairi,
-Yana son cigaban dan uwansa,
-Baya ganin kyashi akan cigaba/nasarar dan uwansa(musulmi)
-Baya Qin taimakon mutum matuqar yanada abunda akazo nema.
-Baya bibiyar mutum akan saiya gano aibunsa/laifinsa,
-Yana kyauta taban mamaki
-Bashida rowa,
Wa'yannan kadanne daga cikin kyawawan halaye na manzo S.A.W da dayawanmu muke alaqanta kanmu da ma'abota bin sunnarsa(ahlussunnah)
Nidakai saimu yimakanmu adalci akan shin:
-muna koyida wa'yannan kyawawan  halayennasa?
-muna daukar mutuncin 'yan uwanmu da muhimmanci?
-muna sakin fuska idan mukaga 'yan uwannmu?
-a masallaci kadai ake koyida manzon Allah S.A.W
اللإسلامية،إحترام أهل السبق والعلم والفضل،ومذا احترام الصغير للكبير،ومعرفةأقدارالناس يتفاضلون بالإسلام،والعلم والتقوى،لابالحسب والنسب والمال.
والله الموفق.
Allah ya'azurtamu da jin tsoronsa hakikanin jin tsoronsa,wanda acikin hakanne zamu samu dukkan halaye da dabi'u irin wanda Allahn yakeso kuma yake yabon masu su.


Friday, June 28, 2019

DUK WANDA KAGA YA KAUCE HANYA BA DARIYA ZAKAYIBA

Sau dadama idan mutum yaganshi cikin masu yin abunda yakamata(masu bin dokokin Allah) sai yadauka duk wanda bashiba halakakkene.
Eh tabbas duk wanda yabijirema hanyar Allah ya halaka matuqar ya mutu akan wannan mummunar hanya.Amma kai idan kaga wani ahakaba dariya zakayi ba.
Kaima ba dabararka bane dacene daga Allah.Kuma ka himmatu afili da boye wajen son kaga yadawo hanya,ta hanyar yimasa addu'a tsakaninka da Allah agaban idonsa da bayan idonsa.
Idan kasamu dama kuma sai kajawo hankalinsa akan tsayin abunda yake aikatawa.
Domin indai yazama dabi'ar mutumne tattauna matsalar wani ta bangaren  aibatawa,ko kuma kayita bibiyar mutum saika gano laifinda yake aikatawa kawai dan aibata wannan mutum to tabbas kaima akwai yiwuwar Allah yajarabceka da wannan aikin.
Sai bincike don yanke hukunci misali ga alkali akan wani mutum,ko wani maisasanci yabinciki yadda abu yafar tsakanin mutanen da suka samu rashin jituwa Dan samun maslaha shima ba laifibane.
 Rike sirrin dan uwanka musulmi yanada matuqar mahimmanci koda yaushe mudunga kyautatama 'yan uwanmu zato.Allah yasa mudace.Ameen

Wednesday, June 26, 2019

GYARA KAYANKA

Bayaushe yana karin magana dayake cewa;
Girman kai rawanin tsiya.
To tabbas wannan abu haka yake,domin shi girman yana jawo abubuwa marasa dadi ga ma'abocinsa.Kadan daga cikin illar girman kai akwai:
-yana sa maishi yakaskantar da duk wanda bashiba
-yanasa maishi ganin girman kanshi fiyeda kowa
-yanasa kafircema ni'imar Allah
-yanasa kin karbar gaskiya ko aiki da ita
-yanasa jiji dakai
-yana haifarda gaaba
-yana haifarda hassada
-yana haifarda izgilanci ga bayin Allah akan matsayin dashi Allah ya'ajiyesu
-yanasa mutum yarasa imani
-yana jawoma maiyinsa halaka
-yana haramta maishi shiga aljannah
-yana sabbaba shiga wuta
Saboda manzon Allah S.A.W yayi bayanin abunda ake cema girman kai cikin kalmomi guda biyu:
1-Raina mutane da
2-Qin gaskiya
Duka matsayin daka samu kanka karka sake ka raina mutum,sau dayawa zakaga mutum cikin 'yan uwansa ko cikin abokai idan Allah ya daukakashi saikaga duk wanda baida matsayi irin nasa bai ishesa kalloba.saiya dunga ganin kaskancine yaje yaziyarci yar uwarshi/dan uwanshi want,cibayane yakaima abokinashi want saboda wani abuda Allah yahore masa.
Bayan mazon Allah S.A.W yace:ya ishi zama laifi agaban Allah mutum yajema Allah ya qasqantarda dan uwansa musulmi.
Allah yatsaremu da girman kai,domin shine yake hana mutum karbar gaskiya saboda yana ganin Kamar duk wanda zai fada masa gaskiya baikai matsayin dazai fada mashiba. 

Monday, May 20, 2019

ALAQAR MUSULMI DA RAMADAN 2

Karka yarda azuminka yaqi samun kar6uwa wajen Allah.
Hakika azumi yana daga cikin manyan ibadun Allah,shiyasa hadithi yatabbata daga manzon Allah S.A.W wanda Imamu Muslim yafitar dashi
من صام يوما في سبيل الله باعد الله بذلك اليوم وجهه النار سبعين خريفا.
Ma'ana : duk wanda ya azumci wani wuni saboda Allah,Allah zainisanta fuskarsa(zai nisantashi) daga wuta tazarar nisan shekaru 70 tsakaninshi da'ita.
Haka imamul Bukhari ya fitar da hadithi:
إذادخل رمضان فتحت أبواب الجنة،وغلقت أبواب جهنم وسلسلت الشياطين.
Ma'ana:dazarar Ramadan yashigo Allah cikin hikimarsa da ikonsa yanasa abude kofofin aljannah,ana rufe kofofin jahannama na kuma daure kangararrun shaidanu.
Mai azumi yana shiga aljannah tawata qofa tamusamman(Rayyan)
TO AMMAFA MANZON ALLAH S.A.W YA FADA CEWA:DAYAWA ANA SAMUN MAI AZUMI BAYA SAMUN KOMAI AMATSAYIN LADA/SAKAMAKON AZUMINSA ,SAI DAI KAWAI YA SHA YUNWA DA QISHIN RUWA KAWAI.Kenan yayi azumin amma Allah bashida buqatar azuminsa don haka bai kar6a ba.
WACE ASARA TAFI ACE YADDA AKE WANNAN IBADA MUHIMMIYA ACIKIN IRIN WANNAN LOKACIN DAMUKE CIKI NA TSANANIN ZAFIN RANA ,ACE BA'A KARBI AZUMIN MUTUMBA.ANYA AKWAI ASARAR DATAFI WANNAN?
DAGA CIKIN DALILAN DAKE IYASA ALLAH YAQI KARBAR AZUMIN MUTUM AKWAI:
1-Qarya,
2-Sata,
3-Giba,
4-Annamimanci,
5-Ha'inci,
6-Maganganun banza(batsa)
7-Kallon finafinan bats a
8-Qasqantarda dan uwanka musulmi,
9-Qintaimakon wanda kasan yana buqatar taimakonka,bayan kanada halin taimakon
10-Zage-zage/fara
11-Hada jiki da mace waddaba muharramarkaba/namijinda ha muharraminkiba
12-Niyyar karya azumi,
13-Yawan koke/magana akan cewa azumin akwai wahala
Dadai sauransu.
Fatanmu da ddu'armu Allah yatausaya mana yakar6a mana azuminmu dasauran ibadunmu.

Wednesday, May 15, 2019

ANYA KUWA DIMOKRADIYYA AKE?

صدق رسول الله صل الله عليه وسل إذقال:أخوف ما أخف على أمتي الأئمة المضلون.

Tabbas manzon Allah yayi gaskiya ,domin yafada cewa:abunda nafijima al' ummata tsoronsa shine jagorori batacci/batattu.

Abunda nalura dashi a Nigeria:
*Musulmi bashida 'yancin magana
*Jami'an tsaro na DSS sun kware wajen kama malaman addinin musulunci
*Ba'ason malamin addini yakasance yana fadin gaskiya ,sai dai rufa-rufa
*Amfison malaman da suke yaqar 'yan uwansu saboda wata jam'iyyar da 80 % zuwa 90% 'yan jam'iyyar da'ake iqirarin bata masu gaskiya bace
*Anfison ana kashe 'yan uwanka kace gyara ake
*Anfi taimakon addininda ba musulunciba
*akullum ba'aso Dan kasa yasan inda ake ha'intarshi
*Jami'an tsaro sunzama karnukan farautar masu mulki
*aduk lokacinda kaji ance ankama wani saboda maganar dayayi domin tana iya jawo rikici, to zakaga musulmine
*Manyan malamai dayawa daga cikinsu sunkoma neman gamsarda masu mulki saboda maslaharsu kadai
Iyakar sanina babu malamin sunnah dayake zuga mutane suyi ta'addanci.
Duk abunda malami zai fada kodai yayi gaskiya kokuma yafadi akasin haka.Sai aduba maganarsa idan gaskiya yafada sai adauki maganarsa domin ayi gyara,idan kuma ba gaskiya bane sai warware maganarsa da hujjoji masu gamsarwa.
Mu abunda muke cewa wa'yannan abubuwan dake faruwa na kashe-kashe rayukan al'umma batareda laifin komaiba sai dan suna musulmai,da agwamnatin bayane wa'yanda suke hana afadi zahirin abunda yake faruwa sunefa suke kuka suna tir da Allah wadai da abunda yake faruwa.
Sai yanzu kuma sai ace abunda yake faruwa baza'ayi maganaba.
Kai mukam mungaji da gafara sa bamuga Qahoba.
Allah Muna tawassuli da ibadar azumi damukeyi,karatul al'qur'ani dasuran ibadu Kaku6utarda bayinka da'aka tsare abisa zalunci,Allah katsare yan uwa musulmi aduk inda duke.Allah kagyara mana shuwagabanninmu.Idan kuma ba masu shir yuwa bane kadaukar mana matakin daya dace akansu.AMEEN


Friday, May 10, 2019

GASKIYA MAI DACI

Azahirin gaskiya akwai matsalolin da alokacin baya basu tsananta kamar yadda ake shan wahala yanzuba
Farkodai yakamata dukkanmu musani cewa tabbas komai yana kasancewane bisa qaddarawar Allah.Idan Allah yaso faruwar abu yana kasancewa kamar yadda yaso batareda gudummuwar kowaba.
Amma hakan baya nuni dacewa duk abunda shuwagabanni sukayi nakuskure sai ace ai haka Allah yaso babu mai iya kawo sauqi sai Allah.Abbas hakane amma;
 menene hikimar hukunta shugabanci?ko shakka babu don maslahar al'ummane.Kai shugaba dole kasani cewa talakawa nada haqqi dayawa akanka,na daga cikin haqqokin:
*tsare masu lafiyarsu,
*Tsare masu dukiyoyinsu,
*tsare masu addininsu,
*Samar da walwala acikinsu,
*Samar masu abunda yake buqtuwane na doke,
Kamar samarda ruwansha,wutan lantarki,samarda magunguna da kulada asibitocin.
Amma kash!!! Al'amarin yanada bantsoro.Azumi al'ummar musulmai sukeyi amma ruwan jarka da'ake saye yayi wahala,da kudinka kan a so kasaya babu ruwan.
Yanzu haka danike rubutunnan munyi awa saba'in da biyu(72 hours)babu wutan lantarki,adai dai lokacin da shuwagabanni basusan da matsalar wuta ko ruwa ba.Tabbas shugabanci ba abu bane mai sauqi,ammafa su sukanema kuma wallahi dukkansu dadin mulkinnan sukeji,abunda yadami talakawa su ba matsalarsubace.
Wannan wani irin canjine?
Anya kuwa masu kare shuwaganni acikin kuskure idan sunyi zasu'iya fuskantar Allah domin bada kariya akan quncin rayuwa da talaka yashiga adalilin sakaci ko nuna halin ko'inkula da shuwagabanni suke nunawa?
Koda yake nidai nagama nazari akan shuwagabanninmu,akwai wanda mune ke sonsu amma wallahi baruwansu da halinda mu talakawa muke ciki,kuma gaskiya zatayi halinta ko anan ko acan zamu gansu afili.
Kana mulki ruwan da talaka zaisha yagagareshi?Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Manzon Allah S.A.W dai yagama addu'a tuni,yace:Yaa Allah duk wanda ka jibintawa wani al'amari acikin al'ummata sai yatsananta masu,yaa Allah katsananta masa wanda kuma yasauqaqa Allah kasauqaqa masa.
Nima har gobe ina akan wannan addu'a.
Allah muna qasqantar dakai gareka katausayamana,kasauqaqa mana,kakarba mana ibadunmu lallai Kai mai ikone akan haka.



Wednesday, May 8, 2019

ALAQAR MUSULMI DA RAMADANA

Ko shakka babu yakamata aga canji arayuwar musulmi acikin ramadana.
Shidai watan Ramadan watane mai falalar gaske domin lokacine da Allah yake yima bayinsa rahma,gafara tareda 'yantasu daga wuta zuwa aljannah.Anaso musulmi lokacin ramadana yakasance mai:
Hakuri
Tausayi
Karamci
Yafiya
Kyauta
Yawan ibada
Karatun alqur'ani
Kame harshensa daga Qarya
Rintse ganinsa
Kiyaye jinsa
Kyautatama iyaye
kyautatama Moqota
kyautatama abokansa
Rufama dan uwansa asiri
Girmama Dan uwansa musulmi
Mai amfanar da jama'a
Sai mutambayi kanmu haka muke?
Saboda mu'amalarmu dayawa tananuna rashin tasirantawa da ramadana,mun dauka azumi shine kawai barin ci dasha da jima'i.
*sai kaga mutum yana azumi amma qarya itace sana'arsa,bayan manzon Allah S.A.W acikin hadithi ingantacce yace:duk wanda bai bar fadar qarya da aiki da itaba to fa Allah bashida buqatar barin cinsa da shansa.
*sai kaga bamu tausayama junanmu,musammam 'yan kasuwanmu sun maida lokacin Ramadan lokaci mafi tsadan kayan masarufi tareda cewa ba kayan bane ke qara tsada.
Sau dayawa saikaga anboya kayan dan asayar da tsada,har qanqara ta ruwa sai kaga ana sayenta Naira 40 #50.
To lallai ya kamata musani manzon Allah S.A.W yayi magana akan matsayin tausayi da kuma sauqaqawa  ga al'umma.
عن عائشة رضي الله عنها قالت:قال رسول الله صل الله عليه وسلم:إن الله رفيق يحب الرفق فى الأمر كله.
Daga Aisha R.A tace:Manzon Allah S.A.W ya ce: Lallai Allah mai tausayine yana son tausayi cikin al'amura gaba daya.Bukhari da Muslim suka fitar da hadithin.
و قال أنس رضي الله عنه،عن النبي صل الله عليه وسلم قال:يسرو ولا تعسرو،وبشرو ولا تنفروا.
Anas R.A yace manzon Allah S.A.W yace kusauqaqa karku tsananta ,kuma kuyi mutane bushara da abu maikyau karku koresu.
وقال صل الله عليه وسلم من يحرم الرفق يحرم الخير كله.رواه مسلم.
Hakanan manzon Allah S.A.W yace duk wanda bashida tausayi ya rasa alkhairi gaba daya.
To mike tunaninmu a irin rayuwar damuke ciki yanzu.Sai kaga wa'yanda ba muba sunfimu son junansu datausayin junansu.amma sai kaga musulmi baya son musulmi Dan uwansa yasamu sauqin rayuwa,koda yanada dalilin dazai taimakeshi bazaiyiba idanma yaga wata hanya da musulmi Dan uwansa zaisamu sauqin rayuwa zai iya hanawa.
Rayuwar damusulmai sukeyi ta wahala da anatausayin juna da ba hakaba da ansamu sauqi,saboda duk wanda kake taredasu kasan Wanda kafi kuma kasan wanda yake buqatar taimako.
Yana daga cikin hikimar farlanta azumi don mawadaci ya dandani irin abunda talaka yakeji dalilin zama da yunwa.Sai wannan yasa masa tausayi dajinqan mai qaramin karfi dayake qasa dashi.
Allah yatausaya mana yakarba mana azuminmu dasauran ibadunmu.Allah yasa mana tausayi dajinqan juna acikin zukatanmu.


Wednesday, May 1, 2019

ILLOLIN ZUWAN MATA WAJEN 'YAN TSIBBU/BOKAYE

Ana samun mata masu yawa da dabi'ar bin 'yan tsibbu da Bokaye saboda manufofi daban daban.
Amma mafi yawa abun dayake kai mata wajen bokaye dalilaine kamar haka:
*jayayyada umurnin Allah
*fada da qaddarar Allah
*sa6ama umurnin manzon Allah
*rashin imani
*rashin tausayi
*hassada
*rashin tawakkali 
Mafi yawan sihirin da mata sukafiyi shine
السحر التفريق:للتفريق بين:
الرجل وأمه
الرجل و أبيه
الرجل وأخيه
الرجل وصديقه
الرجل وشريكه في التجارة
أو التفريق بين الرجل وزوجته،و هذا النوع أخطرها و أكثرها انتشارا
Sihiruttafriq anayin sane don raba:
-Tsakanin mutum da mahaifiyarsa
-Mutum da mahaifinsa
-Mutum da Dan uwansa najini
-Mutum da abokinsa
-Mutum da abokin kasuwancinsa
-Kuma anayi dan raba tsakanin mutum da matarsa,kuma wannan au'in shiyafi hatsari kuma shiyafi yaduwa/shi mata sukafi yawanyi
Babban dalilin mata na fadawa cikin wannan halakar shine KISHI.
Akasarin mata akan kishiya suke halaka.
Wani lokacin uwargidance zakasamu dawannan matsalar,wani lokacin kuma wadda aka auro daga baya itaceke lalata gida.
Mutum yana zauneda matarsa lafiya lokaci daya saikaga yatsaneta,ko sunanta bayaso yaji an ambata,kuma daza'a tambayeshi dalilin dayasa baya sonta shikanshi baisaniba.Duk wace mai wannan mummunar dabi'ar tana  jefa kanta cikin bala'i kala-kala,daga ciki:
*Manzon Allah yace baya tareda ita;
من جنب على امرئ زوجته فليس منا.
أخرجه أبوداود
Manzon Allah S.A.W yace duk wanda yanisanta/yaraba mutum da matarsa to bataya tare damu.
*Allah tana fushi da'ita.
*ba'a karbar sallarta.
*Allah yatsinemata domin ta raba zumunci
*Tanasa mijinta yaqiyin adalci atsakanin matansa,Wanda hakan matsalane agareshi da'ita,
*tana shiga cikin masu annamimanci dukda sihirin datakeyi bai isheta kullum tana yawon hada wannan matarda mijinta,mutanenda taga suna shiri da'ita,yara da babansu wa'yanda ba 'ya'yantaba,
*tana shiga cikin masuyin giba,
*mafi yawa zaka'iske fasiqace saboda mafiyawan 'yan tsibbu da bokayen datakebi sai sunyi lalata da'ita sannan sukeyi mata aikin da take so,
*kodayaushe tana fama da ciwon zuciya saboda ciwon hassada.
*batajin kunyar zagin mutum amma agaban idonsa akasin haka.
*batajin kunyar yin qarya
*koda yaushe baka rabata da laya,ajikin skirt din ta,hannun zanenta,jikin pant din ta,cikin pillow na Maigida dasauran gurare
*komin dadewa wata rana saita baki tausayi saboda duk tsawon lokacinda akadauka tana cutama mijin da matansa lokaci daya abun zai lalace.
*duk gidahen bokaye da 'yan tsibbun datake zuwa batareda izinin maigidanta take zuwaba,mala'iku na tsine mata.
Allah ya shiryi masu wannan muguwar halayyar.

Saturday, April 20, 2019

LETS PUT OUR HANDS TOGETHER AND SAY NO TO OPEN DEFECATION

Open defecation is the human practice of defecating outside (in the open environment) rather than into a toilet. People may choose fields, bushes, forests, ditches, streets, canals or other open space for defecation. They do so because either they do not have a toilet.The practice is common where wastes disposal infrastructure and services are not available. Even if toilets are available, efforts may still be needed to promote the use of toilets.
About 892 million people, or 12 percent of the global population, practiced open defecation in 2016.Seventy-six percent (678 million) of the 892 million people practicing open defecation in the world live in just seven countries.
Open defecation can pollute the environment and cause health problems,like :
-cholera,
-dysentary
-dirrhoea
-Polio
-hepatitis A
-typhoid
-Schistosomiasis/bilharzia
-trachoma
-malnutrition
-intestinal worm
High levels of open defecation are key to
*high child mortality,
*poor nutrition,
* poverty, and
* large disparities between rich and poor.
Actually,I believed that the solution to open defecation requires the involvement of individuals,house holds and government.The government should do the best it can in the provision of adequate toilets and water,there is also a need for education and awareness to correct some negative norms and beliefs of the people.
Its happen to be a common thing to find human faeces around the public areas,even in the cities across the country,as such there is need for a strong penalty on any body fought defecating in an open spaces.
Unarguably,adequate sanitation with good hygiene and safe /clean water are fundamental to good health, social and even economical development.
 Note:to my awareness there no religion in the world that teaches poeaple to pollute their environment,like in Islam its forbidden to defecate by the road,canals(water bodies),or in pubic.
Say no to this inhuman practice.


Wednesday, April 17, 2019

مفاتيح النار للنساء(MABUDAN WUTA GA MATA)

Ya ke 'yar uwa na tabbata
ke musulmace kuma kinyarda da manzon Allah S.A.W,kuma kitabbata cewa duk abunda yafada gaskiyane,to hakika Hadithi ya tabbata daga manzon Allah S.A.W:
Abdullahi Dan Abbas R.A yace:Manzon Allah S.A.W yace :annuna mani aljannah sainaga mafi yawan 'yan cikinta talakawane,kuma annuna mani wuta sainaga mafiya yawan 'yan cikinta Matane.
Haka ma Abi Hurairah da Abdullahi Dan Umar R.A sunfadi irin abunda Dan Abbas yafada suma sunjine daga bakin manzon tsira S.A.W.
 *Ko kinsani 'yar uwa daga cikin abunda yake kai mata wuta akwai;SIHIRI
السحر من مفاتيح النار للنساء،سواء كان القيام بعمل السحر أو الذهاب إلى الساحر وتصديقه.
Sihiri yana daga cikin mabudin shiga wuta ga mata,kodai takasance ita keyinsa da kanta kokuma zuwa takeyi anayi mata to duk dayane.
 Manzon Allah S.A.W yace :duk Wanda yaje yaje wajen mai sihiri yakuma yarda da abunda yafada masa,to ya kafircewa abunda aka saukarwa Muhammad S.A.W.,Dan haka babu makawa maiyin sihiri ko wanda yake zuwa ayi masa yana kafirta.
Shikuwa idan mutum yamutu kafiri babushi babu shiga aljannah.
 Sau dayawa Mata idonsu yana rufewa akan al'amarin kishiya(abokiyar zamanta)saikaga tashiga bin malaman tsibbu(bokaye)duk wani lungu dasaqo idan taji labarin irin wa'yannan batattun saitaje,saboda buqatunta,kadan daga cikin abundance take buqata ayimata sune:
*Zata buqaci asawa mijin qin abokiyar zamanta,
*Zata buqaci amaido hankalinshi kanta kadai,
*yakasance maganarta kawai yake saurare,
*Komin muhimmacin abu idan ba ita tace ayiba to bazaiyiba,
*Tana raba zumuncin miji da 'yan uwansa,
*Tanasa miji yatsani 'yayan daba nataba,
*Dukiyarsa gaba daya tana komawa karkashin ikonta
*Tana fitarda abokiyar zamanta daga cikin gidan.
 wannan kadan kenan daga cikin mugun aikin mata masu bin malaman tsibbu.
Tabbas kyautatawar mace ga mijinta yanasa mijin yaso matar,amma ba irin son dayawuce dabi'a ba.
Saboda sona Allah baya sanya mutum ya dinga bin umurnin matarsa harya sa6awa Allah.Sona Allah bayasa miji yabi ra'ayin matarsa wajen yanke zumunci tsakaninsa da 'yan uwansa,amma agefe daya kuma saikaga shi mijin yana rawar jiki wajen kyautatawa danginta.
Kuma duk laifin daxatayi bazai ta6a ganinsa amatsayin laifiba.
Shiyasa Manzon Allah S.A.W yace
عن ابن مسعود رضي الله عنه قال:سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:إن الرقى والتمائم والتولةشرك
Daga Dan Mas'ud R.A.yace naji manzon Allah S.A.W yana cewa:Lallai Ruqya wadda bata shari'a ba,da daura/rataya laya,guru ko kambu,da sihirinda akeyi domin mallake miji,rabashi da matarsa(bita zaizai)Dukkansu shirkane.
Qarin bayani akan wannan hadithin zaizo arubutu nagaba insha Allahu.sannan kuma zamuga illoli da hatsarin da mace ke fadawa adalilin bin 'yan tsibbu,yaya qarshenta yake kasancewa.Allah yatsare mana 'yan uwanmu mata harma da mazan daga bin wannan mummunan hanya.

Thursday, March 21, 2019

TAIMAKAMA DAN UWANKA MUSULMI DON ALLAH,ALAMANE NA IMANI

Duk cikin aikin imani taimako da dukiya yafi wahala,amma wajen masu imani sunajin sauqin taimakawa da dukiyarsu ahanyar Allah.Wanda yana daga cikin ciyarwa/taimako acikin hanyar Allah taimakama Dan uwanka musulmi wanda kasan cewa yanada buqata ko baitambayeka ba,ballantana kuma idan har ya tambayeka akan kataimaka masa.
Shaidan kuma kullum bayason yaga mumini yana taimako domin yana daga cikin abun dayake kusantar da musulmi wajen Allah shigarda farin ciki azukatan halittun Allah musamman musulmi,idan Har za'ataimaki KARE asamu aljannar Allah ina ga wanda aikinshi kenan taimakawa Dan uwanshi musulmi akan wata buqata dayake da ita/damuwa?
 Kaduba kaga yadda magbata suke aiwatar da imani azahiri;
جاء في تاريخ بغداد؛أن فقيراجاء إلى عبد الله بن المبارك،فسأله أن يقضي عنه دينا عليه سبعمائة درهم.فناوله عبد الله كتابا إلى وكيل ماله فذهب به الفقير،فلماقرأه الوكيل قال للفقير:كم الدين الذي سألت فيه عبد الله أن يقضيه عنك؟قال:سبعمائة درهم،فكتب الوكيل إلى عبد الله أن الرجل سألك أن تقضي عنه سبعمائة درهم،وكتبت له سبعةآلاف درهم،وسوف تغنى الأموال.فكتب إليه عبد الله:إن كانت الأموال قدفنيت غإن العمرأيضاقد فنى،فأجز له ماسبق به قلمي.
Ya zo acikin tarihin Baghdad,wani faqiri (matalauci) yaje wajen Abdullahi Dan Mubarak ,ya roqeshi yataimaka ya biya masa bashin da'ake binsa Dirhami dari bakwai(Dirhami 700)sai Abdullahi Dan Mubarak yarubuta takarda yabashi yakaima maikular masa da dukiya.sai wannan faqiri yatafi dawannan wasiqa(takarda) yakaimasa, Damaikula da dukiyar yakaranta sai yatambayi Faqiri nawane  bashinda kanema yabiya maka? Sai yace Dirhami 700,sai mai kula da dukiyarnan ya sake rubutawa Abdullahi Dan Mubarak cewa shifa mutuminnan bashin  Dirhami 700 yaroqi kabiya masa,kaikuma ka rubuta Dirhami 7000,ai dukiyar tana iya qarewa idan kabashi dirhami 7000.
Sai Abdullahi yasake rubuto ma maikula dakukiyarsa idan dukiya zata qare ai rayuwama tana qarewa,Kawai kabashi abunda narubuta.
 Dirhami 1 dai-dai yake da Naira 98.60,kenan faqirinnan Naira dubu sittin da Tara da naira ishirin(N69,020)ya roqi yabiya masa ,amma yabashi Dirham Dubu bakwai akudin Nigeria N690,200,haka yabashisu saboda Allah batareda ya qasqantar dashiba.
Haka akeso duk lokacin da Dan uwanka musulmi yanemi kataimaka masa to kayi kokari kabashi taimakon da bayan yamagance damuwarsa zai samu abunda zai yi amfani dashi wajen sana'ar da zata taimaka masa da iyalinsa.Wannafa itace 'yan uwantaka amusulunci.Duk lokacin da Allah yahadaka da mutane suka nemi taimakonka sai kaqi taimakonsu kuma kana da iko,to sai Allah yatambayeka,Karka biyema shaidan cewa ai wahala kayi kasamu,shi wannan dayazo neman taimako wajenka daza'abashi zabin yayi irin wahalar dakayi da zaiyi,wahalarka dan uwa ba itace ta azurtakaba ,Wallahi Allah ne ,don akwai masu irin abunda kakeyi/kayi amma basu samu abunda kasamuba.Anan duniyane kadai kakeda damar dazaka taimaki Dan uwanka.
Amma saikaga mutum Allah yarufa masa asiri,saiya dunga gudun yan uwa da abokansa,ko zuwa wajensu saikaga bayayi saboda yana ganin su basu isa yaje yaziyarcesuba.
 Wani bawan Allah yake mani korafi wata rana cewa shi wallahi yana qoqarin zuwa wajen 'yan uwansa zumunci,wani lokacinma yaje ace wai bacci sukeyi,shikuma ko hidimar gidanshi basu zuwa idanba mutuwa akayiba,ballantana kuma suzo masa ziyara haka kawai,sai yake ce Mani shi wallahi kamar yabar zuwa.Sai nace a'a kai kacigaba da zumuncin dakakeyi,ai Allah yasan zuciyarka,nakuma ce masa al'ummace yanzu idan bakada wani abu ahunnunka ba kowa ke kulakaba ballantana yazo inda kake,haka mafi yawa ake.
Allah yasanya mana tausayi acikin zukatanmu,yasa mana ganin darajar yan uwanmu musulmai da abokanenmu acikin zukatanmu.Allah karka ba shaidan dama yasamu galaba akanmu

Friday, March 15, 2019

MANZON ALLAH (S.A.W)KADAI AKEBI IDO RUFE!!!

Wallahil Azeem!!:Allah bazai tambayekaba idan bakabi,malam waneba,ko shehi waneba sannan bazai kamaka dalaifiba idan baka shiga kungiyar Izala ko Dariqa ba.
Amma tabbas Allah zai tambayeka tareda azabtarwa maitsanani idan bakabi manzon daya'aiko makaba,Muhammad swallallahu Alaihi was all am.Sannan kuma Allah zai kaamaka dalaifi idan kaqibin Qungiyar Sahabban Manzon Allah Swallallahu alaihi was all am.
Saboda duk duniya babu wanda Allah ya'aiko maka,wanda kuma dole awajensa zaka koyi addini irin kuma kafahimceshi,kuma idan kayi aikin Allah yakar6a sai Annabin Allah kuma manzonsa Muhammad Swallallahu alaihi wasallam.
قال الله تعالى:هواالذي أرسل رسوله بالهدىودين 
لحق ليظهره على الدين كله وكفى بالله شهيدا(٢٨)
محمد الرسول الله،والذين معه أشدآء على الكفار رحماء بينهم.....(٢٩)
Allah Ta'ala yana fada acikin suratul Fathi ayata 28-29 cewa:Allwh shine wanda ya'aiko manzonsa Annabi Muhammad S.A.W dashiriya dakuma addinin gaskiya(musulunci)don yarinjayarshi akan duk wani addinin dabashiba kuma lallai Allah ya'isa yazama maisheda akan hakan.
 Muhammadu Manzon Allah ne(Allah yana shedawa duniya akan masu qaryata manzoncin annabi S.A.W ,ko sunqi ko sunso Allah ya tabbatar dakasancewarshi manzonsa,wanda yazo dasaqon addinin musulunci )wa'yanda suke taredashi(sahabbansa)basu jiyar dakafirai dadi,basu sassauta mash,amma suna jinqan junansu suna tausayin junansu(suna taimakama junansu,basuson abunda zai jefa 'yan uwansu cikin halin qaqanikayi.......
Duk duniya Manzon Allah kadaine yakamata yazama madubi awajenka ,duk bunqasar malami ana binshine idan abunda yake fada ko yake koya mana yayi dai-daida karantarwar manzon Allah S.A.W.
   Saboda shikadaine binsa yake addini sa6a masa kuma yake jawoma mutum fushin Allah,kamar yadda Allah yatabbatar manada haka,cikin suratu Noor ayata 63
فليحذر الذين يخالفون عن أمره أن نصيبهم فتنة أويصيبهم عذ اب أليم
Masu sa6a umurnin manzon Allah suji  tsoron fitina sakamakon sa6a masa,ko kuma wata azaba mai radadi.
قال الله تعالى:من يطع الرسول فقد أطاع الله و من تولى فما أرسلناك عليهم حفيظا
Duk wanda yayimaka biyayya to tabbas Allah yayimawa,.....
وقال تعالى:وما ءاتاكم الرسول فخذوه ومانهاكم عنه فانتهوا،والتقوا الله،إن الله شديد العقاب(الحشر:٧)
Duk abunda manzon Allah S.A
.W yakawo muku/ya umurceku tokuriqeshi dakyau,sannan duk abunda yahaneku akansa to kuhanu daga aikatashi,kuji tsoron Allah,lallai Allah mai tsananin uqubane akan masu sa6ama umurnin manzon Allah
Kaf duniyar nan babu Wanda akaba saqon addinin musulunci sai manzon Allah,kuma ya'isar dasaqon Allah.
Wallahi babu wani abu acikin addini da idan aka aikatashi za'asamu lada fache saida manzon Allah yayi bayaninsa.
ADDININ ALLAH YAGAMA CIKA TUNKAFIN MANZON ALLAH YABAR DUNIYA,ALLAH YATABBATAR DAHAKAN.
Kuma dole saikayi Ibada yadda manzon Allah S.A.W yayi sannan zaka samu ladar abunda kayi wajen Allah.
Muhadu arubutu nagaba;Ba malam,wane,ko shehi wane aka aiko makaba.
Allah yadatardamu dabin sunnar manzon Allah  S.A.W.


Tuesday, March 12, 2019

SUGABANCIN QASATA NIGERIA

 Kai talakan Nigeria wallahi yakamata kadawo hayyacinka,dangane da qoqarin ganin ka 6ata ma wani rai akan shuwagabannin da mafi yawa batakai sukeba.Ko addini kakeyi don ka6atama wani rai to bakada lada.Amma abun mamaki dayawa daga cikin talakawa idonmu ya rufe akan wani wanda wallahi idan za'a rasaka bazaiji ko ajikinsa ballantana yaji damuwa indai har rasaka zaisa yacimma manufarsa.
 Abun mamaki wani lokacin saikaga harda malamanmu,basu auna maganganun dasuke furtawa akan siyasa dakuma Dan siyasar Nigeria.Tayadda zakaga/zakaji malami yana fadin maganganunda mai ilimin addini kuma akan fahimtar magabata nakwarai baikamata yana yinsu.Bayan duk ta bayyana babu irin rashin gaskiyarda kiwane Dan jam'iyya bayayi hasalima mafiyawan wa'yanda ake tsarkakewa abunda yayisu shiyayi wa'yanda ake zagi.
Ni haryanzu abunda kasa yarda dashi shine duk cewa duk Dan jam'iyyar su wane duk lalacewarsa,duk rashin gaskiyarsa indai Dan jam'iyyajam'iyyar wanene/suwane mutumin banzane.Shikuwa wanda baya cikin jam'iyyar suwane koda ya fi Dan jam'iyyarsu wane nagarta.
Nidai abunda nasani wanda yake saman mulki yafi damar yin magudi sama da wanda yake bashida mulki.
Kuma indai gaskiya da adalci za'ayi mutum bazai dage ala dole saiya zarce kuma kotawane hanya.
Amma tabbas yakamata mudawo mufuskanci gaskiya,babu laifi kayautatama mutum zato kuma dunga yabonshi akan kyawawan halayensa,amma hakan bai bude kofar shiga gaban Allah da manzonsaba,wajen magana da aiki kamar yadda Allah Ta'ala yafada acikin littafinsa mai tsarki:
يأيها الذين أمنواولا تقدموابين يدي الله ورسوله واتقوا الله،إن الله سميع عليم(١).
Allah ya fada cewa:ya ku wa'yanda kukayi imani(kuka bada gasikiya da Allah),karku shiga gaban Allah damanzonsa akan wajen furta wani abu aikata wani aiki acikin addinin musulunci,kuji tsoron Allah lallai Allah mai jine akan duk abunda kuke furtawa kuma mai cikakken ilimi akan duk abunda bayinsa suke aikatawa afili da boye.
 Don haka lallai mudinga taka tsan-tsan akan tsarkake kawunanmu,Domin shi Allah shikadaine yasan abundake fili da 6oye,masanin abun dayake cikin zukatan bayinsa.Tabbas akwai nagartattu acikinmu amma abudake namu shine mukyautata masu zato,tahanyar cewa da'alama wane waliyin Allah ne,tahanyar la'akarida halayen waliyyai dayakedasu cikin irin siffofinda Allah ya fada ko manzonsa S.A.W.Amma sai kaji wani harmada rantsuwa cewa wane waliyyine.Maimakon yace Wallahi duk wanda yasiffantu da siffofin waliyyai da Allah yabayyana ko manzonsa ,Wallahi waliyyine.Allah ya fada awani bangaren ayata 32 cikin suratul Najmi
فلا تزكوا أنفسكم،هو أعلم بمن اتقى.
Allah yana cewa karku tsarkake kawunanku shi Allah shine mafi sanin maijin tsoransa.
 Kawai ayi gaskiya aba jama'a wanda suka za6a,tundadai ba wahayi akayiba akan dole sai dan jam'iyya kaza yaci za'a bada mulki,shikuma dan jam'iyyar adawa idan yaci sai ayi amfanida "inconclusive ".
 . Wai anmaida shugabanci business din dayafi tara/kawo kudi masu yawa.
INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'OUN!!!

Monday, March 11, 2019

DAGA QIN GASKIYA SAI BATA!!!!

Sau dayawa idan mu yana rufewa tayadda sai ayi rashin gaskiya amma kuma maimakon wanda yayi rashin gaskiya abashi rashin gaskiyarsa sai aqirqiro wata qa'aida dandai atabbatar darashin gaskiya.
 Kamar yadda kowa yake bibiyan zabe/sakamakon zaben Kano ansan duk abunda yake faruwa har irin mummunan laifin dawani babban jami'in gwamnati yatafka wanda inda umurni za'abi kamar yadda shugaban kasa yabayyana da yayita rayuwarsa.Amma amaimakon wannan aika aika yazama abunda zai tabbatarda kasawa ta jam'iyya mai mulki a kano sai laifin yazama matakin dazai qara basu damar shirya abunda suke shirin shiryawa.
 Shifa mai abun fada baya fada,idan kuma har jam'iyyar adawa zatayi magudi amma babu wanda zai gane laifin da akayi sai "deputy Governor" to lallai akwai lauje cikin nadi.Idan kuma har amatsayinshi na mataimakin gwamna yaga wani rashin gaskiya da'akayi sai mutambayi kawunanmu:
-Ya kamata yazo yakwashe result dindin/votes?
-Ya kamata ahukunta wanda bashi yayi laifiba dalaifin marar gaskiya?
-Magana yakamata yayima wanda alhakin abun yake awuyansu ko kuwa shi doka tace yadauki mataki dakansa?
-Sannan meyatsayar dasakamakon haka har zuwa wannan lokacin?
-meke tunanin mutane idan dan jam'iyyar adawane yayi wannan katobarar?
-Anya anason kamanta adalci kuwa?
Komadai menene ita gaskita dayace tak daga kinta kuma sai bats.baikamata ace jagorori sune ke hura/rura wutar da zata iya janyo tashin hankaliba atsakanin mutanen da ake jagoranta.
Allah Ta'ala yana fada cewa kada qiyayya tasaku kuqi yin adalci/kin fadin gaskiya/aikata gaskiyarba,Allah yace kuyi adalci shine yafi kusada tsoron Allah.
Sannan Allah yace kufadi gaskiya koda akan kankune kowa'yansu nakusa daku.Saboda haka indai don al'umma akeyi to bai kamata abunda al'ummar suka zaba ahanasuba KO kuma ayi qoqarin kwace masuba.Kuma lallai yakamata wanda akejin maganarsa yayi magana tun kafin al'amari ya runcabe,wannan shine dattako kuma shine,adalci sannan kuma shine riqon amana.Daman shi adalci shine ajiye komai inda yakamata.
Nidai kam dukda ba masanin sha'ar qasa bane amma tunanina ya bani cewa it ita inec wuqa da nama duk ahannunta take,duk wani rashin adalci daza'ayi tofa idan Inec bata bayarda hadinkaiba bazai yiwuba.Don haka cewa asake yin zabe nanda sati uku masu zuwa a Nasarawa tabbas bashine hangar dayakamta abiba,saboda kenan shi mailaifi yasamu yadda yakeso kenan,mafi sharrin shugaba shine wanda mutanen dayake jagoranta bash sonshi amma shi yacije saiya mulkesu.
Kuma babu jam'iyyar idan akaqi zabanta ansabama Allah ba,indai batareda wani daliliba.Inec Kuji tsoron Allah karku jefa al'ummar Kano cikin rudanifa.Allah yakyauta yataimaki wanda al'umma keso kuma shima idan yaci Allah yabashi ikon kyautata masu kamar yadda suka bashi daman yajagorancesu.Itadai karya fure takeyi bata 'ya'ya.
GASKIYA MAI DACI!!GASKIYA MAI DACI!!

Tuesday, March 5, 2019

RAYUWA DARASINE/CE(SAMU DARASHI DUK DAGA ALLAH NE)

Darussan rayuwa sunadayawa,wani darasin yana dasauki,cikin sauqi sai kadaukeshi,wani darasin kuma akwai wahala kuma yanada wahalar dauka.Sai dai abunda yakamata idan wani yana baka labarin darasinshi to karka qaryatashi karkuma kakusheshi,yikokari kafahimci darasinshi domin maiyiwuwa za'ayima jarabawa akan irin darasinshi.
 Duk wanda zai iya tattauna darasinshi narayuwa dakai to tabbas ya yarda dakai kuma ya amince dakai domin sau dayawa darussan rayuwa suna dauke da sirrin mutum,kuma babu wanda zai bayyana sirrinshi gawanda bayaso.
   Abubuwa dadama sukansa mutum ya tunkareka da darasinshi narayuwa/sirrinshi na rayuwa,kadan daga cikinsu akwai:
1-Soyayya,
2-Qauna,
3-Yarda,
4-Zaton alkhairi,
5-Aminci,
6-Abota,
7-'Yan uwantaka tajini/addini
8-Maqotaka,
9-Fahimtarka wajen son taimako,
10-Damuwarka/kulawarka da jama'a
Idan kuwa hakane to duk wanda yazomaka dawani al'amari akan darasinshi na rayuwa,to cikin abubuwa guda biyar(5)dole asamu daya(1):
-Ko dai yazamo Dan uwanka
-Ko yazama abokinka,
-Ko yazama maqocinka,
-Ko kuma yazama qasanka yake,
-Ko kuma dalibinka.
Duk cikin wa'yannan babu wanda baicancanci kulawarkaba,gwargwadon halinda kake dashi.sannan wajen saurarensa yanada kyau kayimasa kyakkyawan fahimta.Akwai inda'yar shawara kadan yake bukata daga wajenka amma idan kajuya masa baya sai yakasa kaiwa ga inda yakeson kaiwa.Akwai kuma wanda alfarmar dayake nema wajenka idan kayi mashi babu abunda zaka ragu dashi amma sai shaidan yayi tasiri acikin zuciyarka yahanaka sanya farin ciki acikin zuciyar bayin Allah,wanda adalilin taimakama wani wajen yayewar damuwarsa/bakin cikinsa kaima Allah zai yaye maka damuwa/bakin cikin ranar alkiyama,kamar yadda manzon Allah S.A.W yafadi haka acikin ingantaccen hadithi.To shikuma shaidan yana bakin cikin mumini yasmu farinciki ranar qiyama.
Abun farko dayakamata kasa aranka duk lokacin dawani yazo da wani darasinshi na rayuwa,KAYI QOQARI KA QADDARA ACIKIN ZUCIYARKA CEWA DA KAINE KAKE CIKIN DAMUWAR DAYAKE CIKI KUMA BAKA DA HANYAR DAKAKE HANGEN YAYEWARTA AKUSA YA ZAKAJI.
KO KUMA DA KAINE KAKE NEMAN SHAWARA AKAN IRIN DAMUWAR DAYAKE CIKINTA KUMA YAKE NEMAN SHAWARAR DAZAI SAMU MAFITA,YA ZAKAYI?
Ataqaice duk lokacin dawani yazo maka dadamuwarsa/neman shawararka akan halin dayake ciki,to kajigina damuwarshi dakanka, idan Kaine awannan halin yaya zakaji.
Sau dayawa muna da dabi'ar idan dan uwanmu yazo mana dawata buqata/damuwa sai mununa masa kamar rashin imanine /rashin hakuri,a'a ba haka al'amarin yakeba,Abi Huraira R.A ya ruwaito hadithi wanda Imam Muslim yafitar dash:
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال:خرج رسول الله صل الله عليه وسلم ذات يوم  فإذاهو بأبى بكر و عمر-رضى الله عنهما-فقال:ما أخرجكما من بيوتكما هذه الساعة؟.قالا:الجوع يا رسول الله.قال:وأنا،والذى نفسي بيده،لأخرجنى الذى أخرجكما.قوما !فقاما معه،،فأتى رجلا من الأنصار.....الى أخ
Daga Abi Huraira R.A yace:manzon Allah S.A.W yafita wata rana,sai ga Abubakar da Umar R.A.M,sai manzon Allah yatambayesu meyafito daku daga gidajenku a irin wannan lokacin?.Sai sukace:Yunwa tafito damu ya manzon Allah.Sai yace:nima,na rantseda wanda raina ke hannunsa,abunda yafito daku shiyafito dani daga gida(yunwa).Sai manzon Allah S.A.W yace: kutashi mutafi,sai sukatashi taredashi suka nufi gidan wani ansar,mutumin madina(Abu Haitham ibn Attayyihan R.A)....
Abun lura yadda manzon Allah yunwa tafito dashi daga gida tareda sauran Abokansa kuma Khalifofinsa ,nantake manzon Allah yace sutafi gidan wannan Sahabi don susamu abunda zasuci,kuma dasukaje yayi masu liyafa,har dabba yayanka masu,sukaci sukasha suka godema Allah.Dan haka duk wanda Allah ya hadaka dashi tofa yanada wani hakki akanka kaima kanada hakki akansa.
Yi kokari kazama kamar wannan sahabi mai girma dayaciyar da fiyayyen halitta S.A.W da abokansa su biyu,wajen sharema Dan uwanka kukansa.Allah yaqara mana son juna,da son taimakon juna.Allah yagafarta mana laifukanmu.

Sunday, March 3, 2019

MUHIMMANCIN SALLAH (2)

Saboda muhimmancin sallah,Allah Ta'ala ya:
*Farlanta ta ga manzonsa S.A.W acan saman samata bakwai,acikin awaje madaukaki wanda babu wani wanda zai iya kaiwa/zuwa wajen cikin halittun Allah Ta'ala.
  *Sannan Allah ya farlanta ta ga manzon Allah S.A.W,acikin mafificin dare arayuwar manzon Allah S.A.W,shine daren mi'iraji,wanda cikinsane aka hauda Manzon S.A.W zuwa cikin sammai,tun daga sama ta daya,ta biyi,ta uku,ta hudu,ta biyar,ta shida da sama ta bakwai.wanda manzon Allah yaga abubuwan ban al'ajabi wanda shikanshi mala'ika Jubrilu A.S saidai yajira manzon Allah yawuce can qololuwar sama tabakwai.
  *Yana daga cikin abunda yake nuna muhimmancin Sallah,Allah ya farlanta ta zuwa ga manzonsa S.A.W,ba tareda wasidaba atsakanin Allah da manzonsaba,ai kaitsaye manzon Allah akaba ita,sabanin sauran ibadu Mala'ika jubrilu shiyake kawoma manzon Allah S.A.W.
  *Farkon al'amari Allah ya farlanta salloli 50 akan bayinsa acikin dareda wuni(kwana1).wanda hakan yake nuna yadda Allah yake sonta,wanda bayan manzo S.A.W ya dawo samata 6 ,sai Annabi Musa A.S yakoma arage al'ummarsa bazasu iyayintaba haka,hardai ta dawo sallah biyar(5)kamar yadda akeyinta yanzu.wanda yana cikin falalar Allah darahamarsa salloli biyar akeyi amma kuma amizani ladar salloli 50 ne,wannan tabbas yana daga ni'imar Allah akan bayinsabayinsa,kenan kowace sallar farilla guda daya amatsayin salloli goma take.
  *Haryanzu saboda muhimmancinta Allah yawajabta tsarki acikin sha'aninta,tundaga karamin hadathi da babba(rihi,bawali,bayan gida,fitar maziyyi ko maniyyi ko kuma janaba),hakanan tsarkake najasa ajiki,tufafi dawajen daza'ayi sallah.Saboda masallaci(maiyin sallah) yakasance cikin hali na kamala cikakke,ai yakasance cikin tsarki zahirinsa da badininsa.
*Yana daga abunda yake nuna muhimmancinta yadda nassoshi sukazo dayawa acikin littafin Allah da Sunnar manzonsa S.A.W akan sha'aninta.
*Mutum yana kasancewa adalilin sallah,mai tsarkin jiki dakuma tsarkin zuciya,har lokacin da mutum zaishiga sallah yatsaya agaban mahaliccinsa,yana mai tsarkin zuciya,tsarkin jiki dakuma tsarkin wajenda mutum yakeyin sallar.
Duka wa'yannan suna nuna mana muhimmacin sallah,da matsayinta awajen Allah Ta'ala.
Arubutu nagaba inshaa Allah zancigaba akan falalar sallah da fa'idar da maiyinta yake samu.
   Allah yabamu dacewa.
سبحانك اللهم ربنا وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك

MUHIMMANCIN SALLAH

Ko shakka babu sallah tanada matsayi da muhimmanci maigirman gaske awajen musulmi,yana daga muhimmancinta:
*Sallah tana daya daga cikin rukunan musulunci,kuma tana matsayi na biyu daga shahadatain(Shaidawa babu abun bauta dagaskiya sai Allah,da shaidawa lallai annabi Muhammad manzon Allah ne)kuma itace rukuni mafi girma bayan shahada.
*Kuma sallah itace ginshiqin addinin musulmi,kamar yadda manzon Allah S.A.W yafada acikin hadithi sahihi,wanda Imam Attirmizi yafjtar dashi
قال رسول الله صل الله عليه وسلم:رأس الأمر الإسلام،وعموده الصلاة،وذروةسنامه الجهاد.
Manzon Allah S.A.W ya ce:kai na al'amari shine musulunci,kuma ginshiqinsa shine sallah,tsororuwarsa (qarshensa)jihadi.
Wannan hadithi nafiyayyen halitta S.A.W cike yakeda hikima domin kamar gidane/daki ,idan babu bango to baza'a iya rufe gidanba har azauna ciki,ko kuma gini idan aka cire ginshikinshi to saman zai fado.hakanan itama sallah idan musulmi bayayi to musuluncinsa zai fado(zai lalace)

*Sallah ita kadaice atsakanin sauran rukunan musulunci bayan shahadatain(Kalmar shahada),idan mutum yabarta yana kafirta,kuma kafirci dayake fitarda mutum daga musulunci.Matsaya biyu akan wanda yabar sallah:
   1.Mutum yabar yin sallah,saboda kasala,ko kuma tozarta sallar tahanyar yinta lokacin da'akaga dama,ko yinta batare da kushu'i,ko natsuwa ba.Amma yana mai tabbatarwa azuciyarshi cewa wajibice wallah,to wannan za'ayi masa nasiha akirashi zuwa yatsaida sallah,yadunga yinta cikin jama'a.idan ya gyara to wannan haka akeso,idan kuma yacigaba akan halin dayake na wulaqanta sallah,to anan malamai sunyi sa6ani,akwai wanda sukace ya kafirta kuma idan ana shari'ar musulunci za'a kasheshi,bakuma za'ayi masa sallahba,sunkafa dalili da fadar Allah Ta'ala:
فإن تبوا وأقاموا الصلاة وأتوا الزكوة فإخوانكم في الدين
Allah yana magana akan mushrikai,idan suka tuba daga kafircin dasukeyi,suka tsayarda sallah,suka bayarda zakka,to sunzama 'yan uwanku acikin addini..
Malamai sukace acikin wannan aya ansa sharadi 3,amma duk al'amarin gudane,sharudan sune kamar haka:
-tuba daga shirka/kafirci/laifin
-tsayarda sallah
-bayarda zakka
Dole sai duka sharudan suncika mutum zaikace Dan uwa acikin musulunci.malamai sunce idan aka Sa sharadi guda days(1) ko sama da (1) akan wani abu,to abunda yake wajibi shine aciki sharudan duka ,idan daya baicikaba to kenan mutum bai cika sharadin da'aka ajiyeba.
2.Idan mutum yabar sallah yana mai inkarin wajabcinta(baiyarda cewa sallah wajibi bace),to wannan kafircine babu shakka,saboda qinyarda da wajabcin sallah ta farilla,kafircine tahanyar qaryata Allah da manzonsa,dakuma muminai.kamar yadda Allah yafada acikin suratul Nisa'i a ya ta 115:
ومن يشاقق الرسول من بعد كاتبين له الهدى ويتبع غير سبيل المؤمنين نوله ماتولى ونصره جهنم وسآءت مصيرا
Duk wanda yasa6awa manzon Allah S.A.W bayan shiriya tazo masa(anyi masa bayani), kuma yabi hanyar da bata muminaiba,Allah yace zamu ji6inta masa abunda yaji6inta kuma musashi cikin jahannama,Allah yace mokomata munana idan takasance jahannama.
Hakanan manzon Allah S.A.W yace lallai abunda yake tsakanin mutum da shirka da karfici,barin sallah.
Insha Allah zancigaba arubutu nagaba.Allah yabamu dacewa,yagafarta mana.

Thursday, February 28, 2019

JARABAWAR RAYUWA,QIYAYYA KO SOYAYYAR ALLAH GA MUMINI?

Allah Ta'ala ya halicci bayinsa,kuma ya fifita wa'yansu bayin akan wa'yansu.Amma ana gane soyayyar Allah akan bawansa tahanyar:
Kyawun halitta?,
Tarin dukiya?,
Sarauta?,
Mulki?
Nasaba?,
Yawan 'ya'ya? .
Koshakka babu Allah yana fifita/son bayine masu jin tsoronsa tahanyar sadarda umurninsa danisantar sa6a masa.
Sannan wani hukunci na Allah yakan jarraba bayinsa domin yatabbatarda masu imanin gaskiya dakuma masu rauni/ko imanin qarya.Kamar yadda yafada acikin littafinsa mai tsarki,suratul Baqarah ayata 213 da ayata 155:
قال الله تعالى:أم حسبتم أن تدخلوا الجنةولمايأتكم مثل الذين جلوامن قبلكم ،مستهم البأساءوالضراء وزلزلواحتى يقول الرسول والذين ءامنوامعه متى نصر الله،الآ إن نصر الله قريب(٢١٤).
Ma'ana :Allah yana fadama manzonsa dasauran muminai ,kuna tsammanin zakushiga aljannah alhalin irin abunda yasami wa'yanda suka gabaceku baizo makuba,tsananin talauci ya shafesu,da rashin lafiya(kamar yadda Dan Mas'ud,Dan Abbas,Mujahid,Sa'eed Dan Zubair dasauran malamai suka fassara ) kuma aka girgizasu girgizawa mai tsanani(ai aka jarrabesu da tsoron makiya/abokan gabansu)saboda  tsananin jarrabawa hartakai manzon Allah dasauran muminai suna tunanin yaushe nasara zata zo masu(bawai suna ganin Allah bazai kawo masu dauki/agaji bane,amma saboda qunci dasuka kasance ciki yasa suke addu'ar samun nasara akusa)sai Allah yace kusaurara!! lallai nasarar Allah akusadaku take(gaf kuke dasamun yayewar musibar dakuke ciki.
ولنبلونكم بشىء من الخوف والجوع ونقص من الأموال والأنفس والممرات وبشر الصابرين.....
Tabbas zamu jarrabeku

dawani abu na tsoro,da yunwa,da tauyewar dukiya da rayuka(mutuwar makusanta,'ya'ya,mata,iyaye,abokai dasauran makusanta),da tauyewar 'ya'yan itace,sai Allah yace acikin wa'yannan musibu idan suka samu bayi ,to kayima masu hakuri bushara.Wanda idan musiba ta samesu saisuce;lallai damansu daga Allah sukafito(shiya haliccesu)kuma tabbas zuwa gareshi zasu koma.
 Akwai ayoyi makamanta wa'yannan dayawa.Sannan Hadithi yatabbata daga Manzon Allah S.A.W:
أشد الناس بلاء الأنبياء ثم الصالحو،ثم الأمثل فالأمثل،يبتلى الجل على حسب دينه،فإنكان فيدينه صلابة زيد قلابة،وإنكان في دينه رقة،جفف عنه،ولا يزال البلاء بالعبد حتى يمشي على الأرض ماله خطيعة
Wanda sukafi samun jarabawa mai girma arayuwa, sune annabawa,sai salihan bayi,sannan hawa -hawa(gwargwadon imanin mutum gwargwadon jarabawarsa arayuwa)Allah yana jaraba bawa gwargwadon addininsa(imaninsa)idan bawa yakasance mai qarfin imanine sai jarabawar taqara qarfafa imaninsa,idan kuma yana da rauni sai jarabawar ta'inganta masa imaninsa,bawa mumini bazai gusheba Allah yana jarabashi har sai yakai yana tafiya asaman qasa bashida zunubi kokadan
قال رسول الله صل الله عليه وسلم:مايزال البلاء بالمؤمن والمؤمنة في نفسه وولده وماله حتى يلقى الله تعالى وما عليه خطيئة.
Hakanan imam Attirmizi Rahimahullah yafitar da hadithi manzon Allah S.A.W yace:Mumini ko mumina bazasu gusheba cikin bala'in rayuwa(jarabawa)acikin jikinsa,da 'ya'yansa da dukiyar(talauci ko asarar dakiya) har mutum yahadu da Allah bashida laifi kokadan.
Dan haku yaku 'yan uwa masu imani,karmudinga jin munfi wa'yansu dan Allah yasa munada wani abu ahannunmu,kamar yadda rayuwar yanzu ta koma idan bakada kudi kai ba kowa bane kuma bakada mutunci.idan kanada wani abu kuma komai lalacewarka to za'a dunga mutuntaka.wadata da talauci duka jarabawane.Kasancewarka cikin:
Walwala,
Wadata,
Matsayi na muqami
Baya nuna cewa kafi wane/suwaneba awajen Allah,ko kadauka kai kafisu kusanci da Allah.A'a ganin damar Allah ne.
Idan har kanacikin Wanda Allah yawadata yi amfani dadamar wadatarka kafin rashin damar,Kataimaki bayin Allah matuqar kasamu iko,Kamar yadda manzon Allah S.A.W yace duk cikin mutane babu wani danafi amfana da dukiyarsa kamar Abubakar R.A. kaga kuwa da imani shiyakesa atara dukiya da kuwa duk duniya cikin halittun Allah baza'a samu wanda yafi manzon Allah S.A.W tarin dukiyaba.
Allah yabamu ikon cin jarabawar dayake yimana,yaqara rufa mana asiri,yagaafarta mana laifukanmu.

Saturday, February 23, 2019

KARMU MANTA DA 'YAN UWANMU DAKE YANKIN BATSARI,JIBIYA,SAFANA DA ZAMFARA

AL'UMMA MUCIGABA DASANUA 'YAN UWANMU CIKIN ADDU'O'I,SABODA HALIN DASUKA TSINCI KANSU.BABU SHAKKA AKWAI TADA HANKALI MATUQA MUTUM YANAJI YANA GANI ZAMA CIKIN GARINSU YAGAGARESHI,SABODA MUMMUNAN HALIN DASUKA SAMU KANSU ACIKI NARASHIN AMINCI.
ALLAH MUNA ROQONKA DON QARFINKA DA BUWAYARKA DUK MASU HANNU ACIN JEFA BAYIN CIKIN TASHIN HANKALI DA DAMUWA ,ALLAH KAYI MAGANINSU TAHANYAR DAKASO.IDAN MASU SHIRYUWANE ALLAH KAFAHIMTAR DASU HATSARIN DASUKE CIKI KAKUMA SHIRYAR DASU.
 SANNAN MUDAI ANAN ALHAMDU LILLAH,ANAYIN ZABE(VOTING)LAFIYA,ALLAH YASA KO'INA AYI LAFIYA AGAMA LAFIYA,ALLAH KATABBATAR MANA DA ALKHAIRI,DUK WA'YANDA KAZABA MANA KATAIMAKESU WAJEN KAMANYAWA,DA ADALCI.


Friday, February 22, 2019

BABU MAGANAR SAK!!

Babu maganar sak,idan har muna son cigaba aharkar siyasa.Gobe idan Allah yakaimu za'ayi za6e,tofa sai mundawo cikin hayyacinmu munzabi wanda yakamata musamman wajen zaben "SENATOR KATSINA CENTRAL" saboda zabene tsakanin Wanda jama'a sukasani da kuma wanda ba'a sanisaniba sai wannan lokacin.
Shifa baisan jama'a ba,su ma jama'ar basu sanshiba.
Shikuwa yasan jama'a kuma alal aqalli ya amfanar da jama'a koyayane,akwai abubuwan daza'a iya gani wanda gudunmuwarsane ga al'umma.Ba ina cewa yayi duk abunda yakamata ace yayi bane,amma gaskiya yafi wanda baya jawo jama'a cikinshi.
  Nidai kam wannan shine fahimtata,kuma idan kace kudi akabani,sai kaje kacewa wanda yabaniyabani,wannan kuma ruwanka,nidai kwabo babu wanda yata6a bani dasunan,siyasa.Idan kuma akwai to sai inji.
   Shidai Dan lawan Katsina yace bashida kudin dazaiba jama'a don suza6eshi amma dai mutum yayi tunani,wallahi sak ba mafita bane wani wajenfa sai anyi angulu dakan zabo.Tunda dai koya ta bayyana gareshi APC ,PDP basa tabbatar DA nagartar dan takara,sai dai,akalli shi dan takaran.Saboda bazaiyu mumaida kanmu gida dawaba,tahanyar cewa duk dan jam'iya kaza nagartaccene ko duk dan jam'iyya kaza ba nagartacce bane.
 Mutum nawa ake yabo,ake ganin cancantarsa amma wai daya fita ya koma wata jam'iyya sai ace yazama mutumin banza,kuma barawone...,sannan mutum nawane yake cikin jam'iyyar da ake kushewa ake cewa barayine amma daya koma wata jam'iyya sai ace mutumin kirkine kuma ba 6arawo bane?
Anya akwai lissafi cikin wannan tunanin namu?,ko kuwa dai wahayi akayine duk wanda yaza6i jam'iyya ko dan jam'iyya zaka ya sa6ama Allah?
Qila kuma anyi wahayine duk wanda yaza6i jam'iyya kaza yazama yazama waliyyi duk yadda yake lalatacce?
Don haka nidai kama aza6en sanetor babu zancen sak,kuma kowa dayake katsina central yayi tunani,domin mafi alkhairin mutane shine wanda yafi amfanar dasu.
Allah yasa ayi za6e lafiya agama lafiya,Allah yazama za6in alkhairi cikin dukkan al'amuranmu,Allah duk mai so ko fatan yahaddasa fitina ko rashin gaskiya acikin za6ennan Allah ko waye/suwe Ka sansu kuma Kai kadai zaka'iya yi mana maganinsu,Allah kayi mana maganinsu tahanyar dakaso kuma kaga dama,lallai Kai mai ikone akan Komai.


Wednesday, February 20, 2019

BAZAIYIWU KOWA YASOKABA ,KAIDAI NEMI SOYAYYAR ALLAH

Idan har manzon Allah swallallahu alaihi wasallam shugaban dayafi kowa cikin halittun Allah Ta'ala:
Gaskiya,
Adalci,
Riqon amana,
Tausayi,
Hakuri,
Jarunta,
Dattako,
Son talakawa,
Iya mulki,
Iya magana,
Ilimi,
Tsoron Allah,
Son musulunci,
Son Allah dama wa'yansu nagartattun halaye ya jagoranci mutane amma ansamu fandararru dasuka bijire masa,wa'yansuma sukace azzalumine Subhaanallah!.
Toh inaga wanda bashiba,wanda arashin uwane akanyi  uwar daki.
  Aqa'idar musulunci soyayya bata hana abayyana kuskuren mutum,musamman shugaban al'umma.
 Idan ana maganar adalcin shugabanni na musulunci baza'a taba mantawada ko tsallake Khalifan musulunci na biyuba wato Umar R.A.Saboda takatsan tsan akan dukiyar al'umma Umar R.A,tayadda hatta fitilar gwamnati idan yagama aikin al'ummar dayake jagoranta kashewa yakeyi,saiya kunna tashi domin hidimarsa da iyalinsa.Saboda tausayin Umar R.A wata rana yayi nufin ba wani shugabanci,sai yayi katobara yace shi baitaba sumbatar yaransaba,sai Umar R.A yafasa bashi,yace wannan yanuna bakada tausayi dajin qai.
Lokaci bayan lokaci yana rubuta saqo zuwa gwamnoninsa yana mai gardadinsu akan akodayaushe suzama masuyin abunda yakamata,sukasance masu gaskiya,amana da adalci.Duk Wanda yasamu da zalunci dacin amana yana hukuntashi.Dabba idan tayi tuntu6e hankalin Umar R.A tashi yakeyi,saboda tsoron kar Allah yatambayeshi meyasa baigyara hanyaba har dabba ke tuntu6e.
 Allahu Akbar!! mutane nawa ke mutuwa akan hanyoyinmu saboda rashin kyawun hanya?mutane nawa suke mutuwa adalilin yunwa?mutane nawa ke mutuwa akan rashin kudin magani wanda basutaka karaba ballanta sukarya.
Amma dukda haka Umar R.A idan yana kewayawa don sanin halin da talakawansa ke ciki yanajin qorafe qorafe kala-kala da tuhuma akan baya adalci.Amma duk lokacin dayaji haka ba fada yakeba zuwa yake yaji damuwarsu yayi masu maganinta.
Saboda haka duk wanda akaji yana qorafi idan akan wanda akesone,to kar ayanke masa hukunci akan qiyayyane,a'a tayuwu duk alkhairin da'ake samu shi baije ma saba,tayiwu soyayyar dayakeyima shugaba tasa bayajin dadin yaga anshiga haqqin wani,yanajima wannan masoyinnashi nauyin dayake akansa.
 Mutum nawa kasani suna sa6awa Allah?
Mutum nawa kasani suna sa6awa umurnin Allah?,
Amma bakanuna rashin jin dadinkaba sai sai soki wanda kakeso wanda idan akabi qeqeda qeqe kafishi matsayi awajen Allah.
Akoda yaushe addu'ar alkhairi,da addu'ar shiriya sune suka kamata bakunanmu suna furtawa,amma addu'ar halaka,lalacewa basune alkhairiba koda kuwa abunda mutum yakeyi yayi muni,to farko kayi masa addu'ar shiriya,idan cutarwarsa ga al'umma ya tsananta sai ka roqi Allah yayi maganinsa tayadda shi yaso batayadda kai kakesoba.Kamar yadda Abdullahi Dan Umar R.A yabamu labarin wani hadeethi:
عن عبد الله ابن عمر-رضي الله عنهما:أنه سمع رسول الله صل الله عليه وسلم يقول إذارفعرأسه من الركوع في الركعة الأخيرة من الفجر:اللهم العن فلاناوفلانا،بعدما يقول:سمع الله لمن حمده،ربنا ولك الحمد.
وفي رواية:يدعوعلى صفوان بن أمية،وسهيل بن عمرو،و الحارث بن هشام.
فأنزل الله:ليس لك من الأمرشىءأويتوب عليهم أويعذبهم فإنهم ظالمون(ال عمران:١٢٨).
Abdullahi Dan Umar R.A,wata rana yaji manzon Allah swallallahu alaihi wasallam yana cewa bayan ya dago kansa daga ruku'i acikin araka'ar qarshe na sallar asubahi:Allah yatsinema waane,da waane,bayan yace sami'Allahu liman hamidahu,Rabbana walakal hamdu.Acin wata ruwayar yana la'antar Swafwan ibn Umayyah,da Suhailu ibn Amru,da AlHarith ibn Hishaam.
Sai Allah yasaukar da wannan aya,Al'amarinsu ba ahunnunka yakeba,ko Allah yayafe masu/yakarbi tubarsu,ko kuma yayi masu azaba,tabbas su sunyi zalunci.Ay al'amarin Allah ne kadai zai yanke masu hukunci.Kaga su 'yannanfa suna cikin shugabannin mushrikai ayaqin Uhud,Kuma manzon Allah suka yaqa harsuka karya masa haqori,yakuma la'antarsu sai Allah yadakatar dashi.Kuma sai gashi Sun musulunta.
Don Allah duk wanda akaga ya karkace to abundayafi ataimaka masa da addu'ar shiriya,idan kuma cutarwarsa tayi yawa sai aroqi Allah yayi maganinshi tahanyar dayaga dama.Allah yaqara fahimtar damu,yagafarta mana laifukanmu,yasa mugama daduniya lafiya.

Monday, February 18, 2019

KAGUJI YADA JITA-JITA

يآئيهاالذين ءامنواإن جآءكم فاسق بنبإ فتبينوا أن تصيبواقومابجهالة فتصبحوا على مافعلتم ندمين(٦).
Ma'ana:Yaa kumasu imani idan fasiqi yazo muku dawani labari akan wani ko wani abu,to kubincika(kuyi bincike kafin kuyanke hukunci ko kuma kafin kuyarda)idan bahakaba zaku aukama mutane/yanke hukunci akan jahilci,sai kuwayi gari kuna masu nadama akan abunda kuka aikata nazargin mutum ko jifanshi da abunda bai aikataba.
وسبب نزول هذه الآية:أسرول الله صل الله عليه وسلم بعث الوليد بن عقبة إ الحارث ليأخذ منهم الصدقات،وإنهم لما أتاهم الخبر فرح و او خرجوا يتلقون رسول رسول الله،وأنه لماحدث الوليد أنهم خرجوايتلقونه خاف،فرخع الوليد إلى رسول الله صل الله عليه وسلم،فقال:يا رسول الله،إن الحارث منعني الزكاةوأرادقتلي.فغضب النبي صل الله عليه وسلم عن ذلك غضبا شديدا،وهم في نفسه أنغزوهم إتاه الوفد قالوا:يا رسول الله،إسمعناأنرسولك رجع من الطريق وخشيناأن مارده كتاب جاءمنك لغضب غضبته علينا دايما نعوذ بالله من غضبه وغضب رسوله.فأنزل الله عذرهم في الكتاب.
Adunqule dalilin saukarda wannan ayar ya farune,lokacin da Manzon Allah S.A.W ya aiki Alwaleed ibn Uqbatu bn Abi Mu'aid zuwaga Al-Harith Ibn Dhirar Mahaifin Juwairiyyah uwar muminai(banul Musdalaq)yakar6o Zakka,Dasuka samu labari cewa Waleed ya taho zuwa garesu sai suka cika dafarin ciki kuma suka fito domin tarbar Dan aiken Dan aiken Allah S.A.W,to jin haka baiqarasaba sai yatsorata yana tunanin zasu cutar dashine,sai Waleed yakoma wajen manzon Allah S.A.W yake cewa manzon Allah AlHarith yahana/yaqi bayarda zakka kuma sunso kasheni dakyar nasha.Sai manzon Allah ranshi yabaci sosai har yana nufin zuwa yayaqesu,saiga baqi sunzo sukace:ya manzon Allah munji cewa dan aikenka da aiko zuwa garemu bai isoba ya koma ahanya,sai mukaji tsoro cewa kar ace mune muka 6ata masa rai,muna neman tsarin Allah daga fushinsa dakuma fushin manzonsa S.A.W sai Allah ya saukarda wannan aya.
-Abun lura yadda manzon Allah S.A.W yatasirantu da abunda aka fada masa afarko har yayi nufin daukar mataki saboda yadda da abunda aka fada masa.
-Duk nagartar mutum ba kowace magana bane idan yada za'a yadda da'itaba musamman akan laifin wani,har sai an tabbatarda gaskiyarta.
 Sannan amatsayinka na musulmin kwarai kaguji mummunan zato akan dan uwanka musulmi,domin sau dayawa sai shi Wanda ake munama zoton yabiyo masu jifarshi da magan ganun da zatone,komada laifinsane to matuqar babu maslaha to haramunne yazama abun tattaunawa.Kamar yadda Allah yafada acikin suratul Hujrat a ya ta 12:
يأيهاالذينءامنوااجتنبواكثيرامن الظن إن بعض الظن إثم،ولاتجسسواولايغتب بعضكم بعضا،أيحب أحدكم أن يأكل لحم أخيه ميت اف كرهت من هو اتقوا الله،إن الله تواب رحيم(١٢).
Ma'ana :Yaa ku masu imani kunisanci dayawa daga cikin zato ,domin lallai dayawa daga zato da'akeyi laifine,karku tsananta bincike akan sai ka gano wani yanada laifi,ko kagogama wani laifi,kuma kar dayanku yadunga gibar Dan uwansa musulmi,sai Allah yace yanzu akwai wanda zaiso yaci naman Dan uwansa bayan ya mutu,Allah yace tabbas zaku kyamaci haka,to kuji tsoron Allah tahanyar nisantar abunda yahanaku dakuma aikata abunda yayi umurni dashi,lallai Allah mai yawan karbar tubane kuma mai jinqai.
  Wannan aya mai girma tana koya mana ladabin zamantakewa tayadda bazakayita bibiyar mutumba don kakamashi da laifi,domin duk mai bin diddigi saiyakama wani da laifi to idan baidenaba shima sai Allah yajarabeshi da irin wannan laifin,abunda yafi shine kadungayi masa addu'a idan kasamu iko dagakai saishi kayi masa nasiha.
*Wata rana anzo wajen Abdullahi Dan Mas'ud R.A dawani cewa mashayin giyane har giyar tana diga agemunsa(amma ba'a ganshi yanashaba)sunanufin ayi masa hukunci.Sai Abdullahi R.A yace:mukam tabbas Allah ya hanamu tajassusi(ayitabin sawun mutum/bincike har sai ankamashi akan laifin dayakeyi nasa6on Allah),sai dai idan wani abu yabayyana afili mutum ya aikata sai muyi riqo dawannan abun daya bayyana wajen hukunta mutum(Abi Dawud:4890)
*Giba kuma manzon Allah S.A.W yace itace ka'ambaci dan uwanka musulmi dawani abu abayan idonsa Wanda idan yaji bazaiji dadiba,sai wani sahabi yatambayi Manzon Allah koda abunda yake fada yana aikatawa?sai manzon Allah yace koda abunda yake aikatawane wannan shine giba(cinnaman mutum)inkuwa baya aikatawa hakakawai ake jifanshi da abun to wannan an qagi qarya anjingina masa kenan dukkansu haramunne .
*Sai shaidar zur(shaidar qarya da zancen qarya)
قال صل الله عليه وسلم:ألا أننبئكم بأكبر الكبائر؛الإشراك بالله،وعقوق الوالدين،ألا وقول الزور،ألا وشهادة الزور،فمازال يكررها حتى قلنا:ليته سكت.
رواه البخاري
Manzon Allah S.A.W wata rana yake cewa sahabbansa :banaa fadamuku mafiya girma daga cikin manyan laifukaba?sau3 yana fadan haka,sai sukace eh ya manzon Allah kafada mana,sai yace:ayima Allah shirka,sai sa6ama iyaye(tozartasu daqin yi masu biyayya)yana kishingide agefen damarsa yafadi wa'yannan,sai yatashi yazauna yace:kusaurara da zancen qarya dakuma shedar qarya,bai gusheba yanata maimaitawa inji sahabbai har saida mukace damadai yayi shuru,saboda yadda sukaga hankalinsa ya tashi kuma yana ta sake qara maimaitawa.
-Shaidar zur shine,mutum yayi shaida akan wani abu/yafadi wata magana akan:
-abunda yasan yadda abun yake amma sai yafadeshi ba akan gaskiyar yadda yasaniba /yafaru,
-abunda baisan gaskiya ko rashin gaskiyar labariba ,amma yadunga watsashi/bada labarinsa kamar gabanshi akayi,
-abunda yasan yadda yake,sai dai anfadeshi ba tahanyar dayafaruba
Don hakadai 'yan uwa muyi takatsantsan wajen yada labari,badashi ko gaskatashi matuqar bamu dayaqini akan abunda muke fada ko ya dawadawa.
Allah yaqara tsare mu daga aikata abunda yahanemu yakuma taimakemu wajen aikata ababen dayakeso,Ya gafarta mana laifukanmu,lallaishi mai ikone akan haka.

Friday, February 15, 2019

KAKIYAYI TOZARTA MUTUM,(MUSAMMAN MUSULMI)

Kanaso kagama daduniya lafiya?
Kanaso alkhairinka ya yawaita?
Kanaso rayuwarka tayi albarka?
Kanaso adunga yima addu'ar alkhairi?
Kanaso ladarka tayawaita?
Kanaso maqiyanka suqasqanta?
Kanaso adunga yima zaton alkhairi?
Kanaso jama'a susoka?
Kanaso Allah yasoka?
Tofa babu makawa saika girmama tareda mutunta mutane aduk inda kahadu dasu,musamman musulmi,musamman dan uwanka,musamman wa'yanda kasani.
Allah dakansa yabayyana mana yadda yakarrama kuma yafifita dan Adam(mutum)akan sauran halittu,cikin fadarsa:
ولقدكرمنابني ءادم وحملناهمفي البترول بمرور ربنا هم من الطيبات وفضلناهم على كثيرممن خلقناتفضيلا(الإسراء:٧٠).
Ma'ana:Tabbas mun daraja/karrama Dan Adam kuma dirashi aka tudu(was a)da'ababen hawan da'aka hore masa,dacikin teku,kuma Allah yace munkuma azurtasu da abubuwa masu dadi,sannan muka fifitasu akan mafiyawa daga cikin abubuwan damuka halitta fifitawa.(isra'i:70).
Hakanan Luqmanul Hakim cikin nasihohin dayakema dansa da'Allah yabamu labari acikin suratul Luqman,bayan yayi mashi nasiha,akan karyayi shirka,yatsaida Sallah,yayi umurni da aiki maikyau,yayi hani daga mummuna yakumayi hakuri akan jarrabawa...,sai kuma Allah face:
ولاتصعرخدك للناس ولا ومش في الأرض مرحا،إن الله لا يحب كل مختار فخور(١٨).سورة لقمان
Ma'ana:karka juyarda kumcinka/fuskarka daga mutane danufin qasqantardasu,karkayi tafiya kana taqama,lallai Allah bayason duk wani mai gairman kai mai alfahari.
أي:لا تفعل ذلك يغضبك الله،ولهذاقال:إن الله لا يحب من كل مختار فخور،أي:مختال معجب في نفسه،فخور:أي على غيره.
Ai karka aikata ha kan,Allah zaiyi fushi dakai matuqar kana wulaqanta mutane,shiyasa Allah yace bayason maitaqama ,ai mai burge Kansas(mai jijida kai),mai alfahari gawaninsa. 
 Asuratul Isra'i haryanzu Allah yana fara:ولا ومش فى الأرض مرحبا إنك لن  تخرق الأرض ولن تبلغ الجبالطولا(٣٧).
Allah yana qara jaddadawa karkayi tafiya acikin qasa kana mai alfahari da taqama,domin duk yadda kake ganin ka kai /ka'isa bazaka iya tsaga qasaba saboda girmanka hakanan bazakai girman tsaunikaba(duwatsu manya).
عن أبي هريرة رضي الله  عنه،عن النبي صل الله عليه وسلم قال:بينمارجل يمشي فيمن كان قبلكم،وعليه بردان يتبختر فيهما،إذ خسف به الأرض،فهو يتجلجل فيها إلى يوم القيامة(البخاري:٥٧٨٩).
Abi Huraira R.A yace,manzon Allah S.A.W yace:wata rana wani mutum cikin al'ummar dasukazo kafiku,yana tafiya cikin tufafi na alfarma yana taqama acikin wannan kayan yana jiji dakai,yana raina mutane,kawai sai Allah yanitsar dashi cikin qasa ma'ana qasa qasa tatsage yafada manzon Allah yace haryanzu yana ta tafiya yana qara nitsewa har ranar alkiyama.
Hakanan Imamu Muslim ya fitarda Hadithi,:
قال رسول الله صل الله عليه وسلم:إن الله أوحى إلي أن تواضعوا،حتى لا يفخر أحد على أحد،ولا يبغى أحد على أحد.
Manzon Allah yana cewa :Allah yayi Mani wahayi dacewa kuqasqantar da kai ga 'yan uwanku musulmai,harya kasance babu wani daya dayake yima wani alfahari akan yafishi mat say I ko wata ni'ima da'Allah yayi masa,kuma  babu wani daya dayake  zaluntar wani dan uwanshi musulmi. 
Hakanan Abi Huraira bada labarin hadithin dayaji daga manzon Allah S.A.W:
أن رسول  الله صل الله عليه وسلم قال:ما تواضع أحدا لله إلا رفعه الله.رواه مسلم
Manzon Allah S.A.W yace: babu wani daya dazai qaskantar dakanshi saboda Allah faace sai Allah ya daga darajarsa.
Don haka yaakai Dan uwa Kasani awani bangare na wani had it hi,manzon Allah yana cewa ya ishi mutum sharri aranar alqiyama yaje gaban Allah yawulaqanta dan uwansa musulmi,
عن أبي هريرة رضي الله عنه،قال:قال رسول الله صل الله عليه وسلم....المسلم أخو المسلم لا يظلمه،ولا يخذله،ولا يكذبه،ولا يحقره،التقوى ههنا،بحسب امرىء من الشر:أن يحقر أخاه المسلم كل المسلم على المسلم حرام:دمه،وماله،و عرضه.
رواه مسلم.
Abi Huraira R.A yace: manzon Allah S.A.W yace:musulmi Dan uwan musulmine:
-kada yazalunceshi,
-Kada yatozartashi(yaqitaimakonsa idan yana neman taimako wajensa kuma yanada iko),
-kada yaqaryatashi/yadunga qaryata musulmi dan uwansa,
-kada yarainashi,kodan yaga Allah ya fifitashi dawata ni'ima yadauka yafishi,
Tsoron Allah anan yake,sai manzon Allah S.A.W yayi nuni zuwa qirjinsa.(tsoron Allah azuciya yace,sai gabobi sutabbatar da gaskiyar hakan ko rashin gaskiyarsa),
Sai manzon Allah yace:ya'isa yazama sharri gamutum,yawulaqanta Dan  uwansa musulmi(ma'ana ko mutum yayi abunda yakamata na ibada, bashida laifin komai amma sai yajema Allah ya qasqantar tareda wulaqanta Dan uwansa musulmi,to wanna laifin ya isa yazama sharri(bala'i)dazai jawo masa azabar Allah).
Manzon Allah yacigaba dacewa awaken kowane musulmi haramunne 
-ya zubar dajininsa,
-yataba dukiyarsa (sai dayardarsa,kuma cikin dadin rai),
-yaci/yataba/yashiga cikin mutuncinsa.
Allah yataimakemu wajen mutunta junanmu dakuma ganin qimarsu,Allah yagafarta mana laifukanmu,Allah yaba yan uwanmu marasa lafiya ,lafiya.Ameen



Wednesday, February 13, 2019

KAKIYAYE HARSHENKA👅

Dan uwa,ko kana lura/kula da abunda yake fitowa daga bakinka?
Ko kaasan Harshenka yana'iya jefaka wuta?
Ko kasan mafiyawan gabar da tafi halakar da mutum Harshene?
قال الله في محكم تنزيله:ولا تقف ماليس لك به علم إن السمع والبصر والفؤادكل أولئك كان عنه مسئولا(سورة الإسراء ٣٦).
Ma'ana ;karka bibiyi/karkafadi abunda bakada ilimi/masaniya/tabbaci akansa,kayi bincike cikin duk abunda zaka fada,saboda jinka ,daganinka dazuciyarka duk za'a tambayeka gamedasu.
قال ابن عباس:أيلا تقل،وقال العوفي:لا ترم أحدابماليس لك به علم،وقال محمد ابن الحنفية:يعني شهادة الزور،
وقال قتادة:لاتقل:رأيت ولم تر،وسمعت،ولم تسمع،وعلمت ولم تعلم،فإن الله سائلك عن ذلك كله.
وقوله:كل أولئكأولئك ،أي:هذه الصفات من السمع والبصر والفؤاد،أي:يسأل العبد عنها يوم القيامة وتسأل عنه وعما عمل فيها
-Abdullahi Dan Abbas R.A yana fada cewa ayar tana cewa karka fadi abunda bakada tabbas.
-Aufi yana fada shima akan ma'anarayar:karka jefi wani daya daga cikin mutane da wata magana da bakada cikakken ilimi akan gaskiyar al'amari
-Muhammad ibn Hanafiya yana cewa:abunda Allah ke nufi shaidar zur(Qarya),
Shikuwa Imamu Qataada cewa yayi:karkace ka gani,alhalin baka ganiba,karkace kaji,alhalin bakajiba,karkace ka sani alhalin bakasaniba,domin lallai Allah saiya tambayeka akan haka.
Ibn Kathir yana cewa akan wa'yannan siffofi,tabbas Allah zai tambayi bawa akansu ranar alkiyama,kuma suma za'a tambayesu akan wanda aka horemasu,kuma za'a tambayesu meya'aikata dasu.
وقال تعالى:مايلفظ من قول إلا لديه رقيب عتيد(ق:١٨).
Babu wata magana dawani mai magana zai furta faace akwai mala'ika atredashi yana kiyaye dukkan abunda yake fada kuma yana rubutawa.
Hakanan Allah yaja hankalinmu acikin suratul infitar:
وإن عليكم لحافظين ١٠ كراماكاتبين ١١ يعلمون ما تفعلون ١٢
Yaa kai Dan Uwa kakula kakame harshenka daga aibata mutane musamman akan abunda bakada tabbas.
  Saboda sau dayawa bawa zaiyi wata magana baya kodamuwa da maganar saboda yana hangen ai qaramar maganace amma ajefashi jahannama adalilinta.
Wata rana Abi Musa ya tambayi manzon Allah :wane musulmine yafi daraja awajen Allah,sai manzon Allah yace:shine Wanda musulmai suka kubuta daga sharrin harshensa da hannayensa.Ai baya curar da musulmai da bakinsa tahanyar yimasa:
Qarya,
Qage/QazafiQazafi,
Giba,
Annamimanci,
Da'abunda yayi kamada wيعدلها 
اعلم أنه ينبغى لكل مكلف أن يحفظ لسانه عن جميع الكلام إلا كلاما فيه المصلحة،ومتى استوى الكلام  وتركه فى المصلحة،فالسنة الإمساك عنه،لأنه قد ينجر الكلام المباح إلى حرام أو مكروه،والسلامة لا يعدلها شيء.
 Kasani Dan uwa dole akan duk wani mukallafi yakiyaye harshensa akan furta maganganu idan ba magana bane dayan akwai maslaha cikin fadanta,kuma duk lokacinda yin magana da barin yinta sukazamo dai-dai wajen maslaha, to asunnance yin shurun shiyafi,domin sau dayawa zakaga maganar dayinta ya halatta ba laifibane amma saita jawo haramun ko abunqi.Don haka babufa abunda yakamo zaman lafiya.
Allah yakiyayemu daga sharrin harsunanmu.