Sau dadama idan mutum yaganshi cikin masu yin abunda yakamata(masu bin dokokin Allah) sai yadauka duk wanda bashiba halakakkene.
Eh tabbas duk wanda yabijirema hanyar Allah ya halaka matuqar ya mutu akan wannan mummunar hanya.Amma kai idan kaga wani ahakaba dariya zakayi ba.
Kaima ba dabararka bane dacene daga Allah.Kuma ka himmatu afili da boye wajen son kaga yadawo hanya,ta hanyar yimasa addu'a tsakaninka da Allah agaban idonsa da bayan idonsa.
Idan kasamu dama kuma sai kajawo hankalinsa akan tsayin abunda yake aikatawa.
Domin indai yazama dabi'ar mutumne tattauna matsalar wani ta bangaren aibatawa,ko kuma kayita bibiyar mutum saika gano laifinda yake aikatawa kawai dan aibata wannan mutum to tabbas kaima akwai yiwuwar Allah yajarabceka da wannan aikin.
Sai bincike don yanke hukunci misali ga alkali akan wani mutum,ko wani maisasanci yabinciki yadda abu yafar tsakanin mutanen da suka samu rashin jituwa Dan samun maslaha shima ba laifibane.
Rike sirrin dan uwanka musulmi yanada matuqar mahimmanci koda yaushe mudunga kyautatama 'yan uwanmu zato.Allah yasa mudace.Ameen
0 comments:
Post a Comment