Monday, February 18, 2019

KAGUJI YADA JITA-JITA

يآئيهاالذين ءامنواإن جآءكم فاسق بنبإ فتبينوا أن تصيبواقومابجهالة فتصبحوا على مافعلتم ندمين(٦).
Ma'ana:Yaa kumasu imani idan fasiqi yazo muku dawani labari akan wani ko wani abu,to kubincika(kuyi bincike kafin kuyanke hukunci ko kuma kafin kuyarda)idan bahakaba zaku aukama mutane/yanke hukunci akan jahilci,sai kuwayi gari kuna masu nadama akan abunda kuka aikata nazargin mutum ko jifanshi da abunda bai aikataba.
وسبب نزول هذه الآية:أسرول الله صل الله عليه وسلم بعث الوليد بن عقبة إ الحارث ليأخذ منهم الصدقات،وإنهم لما أتاهم الخبر فرح و او خرجوا يتلقون رسول رسول الله،وأنه لماحدث الوليد أنهم خرجوايتلقونه خاف،فرخع الوليد إلى رسول الله صل الله عليه وسلم،فقال:يا رسول الله،إن الحارث منعني الزكاةوأرادقتلي.فغضب النبي صل الله عليه وسلم عن ذلك غضبا شديدا،وهم في نفسه أنغزوهم إتاه الوفد قالوا:يا رسول الله،إسمعناأنرسولك رجع من الطريق وخشيناأن مارده كتاب جاءمنك لغضب غضبته علينا دايما نعوذ بالله من غضبه وغضب رسوله.فأنزل الله عذرهم في الكتاب.
Adunqule dalilin saukarda wannan ayar ya farune,lokacin da Manzon Allah S.A.W ya aiki Alwaleed ibn Uqbatu bn Abi Mu'aid zuwaga Al-Harith Ibn Dhirar Mahaifin Juwairiyyah uwar muminai(banul Musdalaq)yakar6o Zakka,Dasuka samu labari cewa Waleed ya taho zuwa garesu sai suka cika dafarin ciki kuma suka fito domin tarbar Dan aiken Dan aiken Allah S.A.W,to jin haka baiqarasaba sai yatsorata yana tunanin zasu cutar dashine,sai Waleed yakoma wajen manzon Allah S.A.W yake cewa manzon Allah AlHarith yahana/yaqi bayarda zakka kuma sunso kasheni dakyar nasha.Sai manzon Allah ranshi yabaci sosai har yana nufin zuwa yayaqesu,saiga baqi sunzo sukace:ya manzon Allah munji cewa dan aikenka da aiko zuwa garemu bai isoba ya koma ahanya,sai mukaji tsoro cewa kar ace mune muka 6ata masa rai,muna neman tsarin Allah daga fushinsa dakuma fushin manzonsa S.A.W sai Allah ya saukarda wannan aya.
-Abun lura yadda manzon Allah S.A.W yatasirantu da abunda aka fada masa afarko har yayi nufin daukar mataki saboda yadda da abunda aka fada masa.
-Duk nagartar mutum ba kowace magana bane idan yada za'a yadda da'itaba musamman akan laifin wani,har sai an tabbatarda gaskiyarta.
 Sannan amatsayinka na musulmin kwarai kaguji mummunan zato akan dan uwanka musulmi,domin sau dayawa sai shi Wanda ake munama zoton yabiyo masu jifarshi da magan ganun da zatone,komada laifinsane to matuqar babu maslaha to haramunne yazama abun tattaunawa.Kamar yadda Allah yafada acikin suratul Hujrat a ya ta 12:
يأيهاالذينءامنوااجتنبواكثيرامن الظن إن بعض الظن إثم،ولاتجسسواولايغتب بعضكم بعضا،أيحب أحدكم أن يأكل لحم أخيه ميت اف كرهت من هو اتقوا الله،إن الله تواب رحيم(١٢).
Ma'ana :Yaa ku masu imani kunisanci dayawa daga cikin zato ,domin lallai dayawa daga zato da'akeyi laifine,karku tsananta bincike akan sai ka gano wani yanada laifi,ko kagogama wani laifi,kuma kar dayanku yadunga gibar Dan uwansa musulmi,sai Allah yace yanzu akwai wanda zaiso yaci naman Dan uwansa bayan ya mutu,Allah yace tabbas zaku kyamaci haka,to kuji tsoron Allah tahanyar nisantar abunda yahanaku dakuma aikata abunda yayi umurni dashi,lallai Allah mai yawan karbar tubane kuma mai jinqai.
  Wannan aya mai girma tana koya mana ladabin zamantakewa tayadda bazakayita bibiyar mutumba don kakamashi da laifi,domin duk mai bin diddigi saiyakama wani da laifi to idan baidenaba shima sai Allah yajarabeshi da irin wannan laifin,abunda yafi shine kadungayi masa addu'a idan kasamu iko dagakai saishi kayi masa nasiha.
*Wata rana anzo wajen Abdullahi Dan Mas'ud R.A dawani cewa mashayin giyane har giyar tana diga agemunsa(amma ba'a ganshi yanashaba)sunanufin ayi masa hukunci.Sai Abdullahi R.A yace:mukam tabbas Allah ya hanamu tajassusi(ayitabin sawun mutum/bincike har sai ankamashi akan laifin dayakeyi nasa6on Allah),sai dai idan wani abu yabayyana afili mutum ya aikata sai muyi riqo dawannan abun daya bayyana wajen hukunta mutum(Abi Dawud:4890)
*Giba kuma manzon Allah S.A.W yace itace ka'ambaci dan uwanka musulmi dawani abu abayan idonsa Wanda idan yaji bazaiji dadiba,sai wani sahabi yatambayi Manzon Allah koda abunda yake fada yana aikatawa?sai manzon Allah yace koda abunda yake aikatawane wannan shine giba(cinnaman mutum)inkuwa baya aikatawa hakakawai ake jifanshi da abun to wannan an qagi qarya anjingina masa kenan dukkansu haramunne .
*Sai shaidar zur(shaidar qarya da zancen qarya)
قال صل الله عليه وسلم:ألا أننبئكم بأكبر الكبائر؛الإشراك بالله،وعقوق الوالدين،ألا وقول الزور،ألا وشهادة الزور،فمازال يكررها حتى قلنا:ليته سكت.
رواه البخاري
Manzon Allah S.A.W wata rana yake cewa sahabbansa :banaa fadamuku mafiya girma daga cikin manyan laifukaba?sau3 yana fadan haka,sai sukace eh ya manzon Allah kafada mana,sai yace:ayima Allah shirka,sai sa6ama iyaye(tozartasu daqin yi masu biyayya)yana kishingide agefen damarsa yafadi wa'yannan,sai yatashi yazauna yace:kusaurara da zancen qarya dakuma shedar qarya,bai gusheba yanata maimaitawa inji sahabbai har saida mukace damadai yayi shuru,saboda yadda sukaga hankalinsa ya tashi kuma yana ta sake qara maimaitawa.
-Shaidar zur shine,mutum yayi shaida akan wani abu/yafadi wata magana akan:
-abunda yasan yadda abun yake amma sai yafadeshi ba akan gaskiyar yadda yasaniba /yafaru,
-abunda baisan gaskiya ko rashin gaskiyar labariba ,amma yadunga watsashi/bada labarinsa kamar gabanshi akayi,
-abunda yasan yadda yake,sai dai anfadeshi ba tahanyar dayafaruba
Don hakadai 'yan uwa muyi takatsantsan wajen yada labari,badashi ko gaskatashi matuqar bamu dayaqini akan abunda muke fada ko ya dawadawa.
Allah yaqara tsare mu daga aikata abunda yahanemu yakuma taimakemu wajen aikata ababen dayakeso,Ya gafarta mana laifukanmu,lallaishi mai ikone akan haka.

0 comments:

Post a Comment