أم المؤمنين ،خير نساء العالمين ،أم القاسم ابنةخويلد،وأم أولاد النبي صل الله عليه وسلام.وأول من آمن وصدقه قبل كل أحد
وهي ممن كمل من النساء ،كانت عاقلة منسوبة بالكرم،من أهل الجنة.
Uwar muminai ,mafi alkhairin mata,mahaifiyar Qaasim diyar Kuwailid,kuma itace mahaifiyar duka 'ya'yan manzon Allah S.A.W.
Kuma itace farkon wadda tayi imani kafin kowane mutum,ana siffantaatada karamci.
Tana daga cikin mata da'akayi atarihin duniya masu cikar kamaala,kuma yar aljannah,kamar yadda manzon Allah S.A.W yafada:
قال أبي هريرة رضي الله عنهأتى جبريل النبي صل الله عليه وسلم فقال:يا رسول الله! هذه خديجة قد أتت معها إناء فيه طعام أوشراب،فإذا هي أتتك فاقرأ عليها السلام من ربهاومني،وبشرها ببيت في الجنة من قصب،لا صخب فيه ولانصب.
صحيح البخار(٣٨٢٠).
Abi Hurairah R.A yace :malaa'ika Jubreelu yazo wajen annabi S.A.W sai yace:yaa manzon Allah S.A.W ! ga Khadijah R.A nan tafe zuwa wajenka,atare da ita akwai kwano cikinsa akwai abinci/abunsha,idan ta'iso wajenka kakaranta mata sallama daga Ubanhinta dakuma ni,sannan kayi mata albishir dawani irin gida acikin aljannah wanda babu hayaniya babu tashin hankali .
Wannanfa Itace Khadijah Allah ya aiko mala'ika cewa Allah yana gaisheta shima kuma Jubreelu A.S yana gaisheta da kuma tabbacin gida acikin aljannah.
Yana daga karamarta Manzon Allah S.A.W itace matar dayafara aure,kuma bayan ya aureta bai hadata wata mataba tsawon she kara 25 har saida rasu sannan ,kuma dukkan 'ya'yansa S.A.W ita tahaifesu.
Ta taimaki manzon Allah da dukiyarta batareda tanayi masa goriba akan duk abunda tayi masa ko tab as a,tana qarfafa masa guiwa akan harkar da'awarsa kamar yadda yazo lokacin da akafara yimasa wahayi ya firgita amma ita tadunga kwantar masa da hankali cewa wallahi Allah bazai tazartaakaba,saboda kana sadarda zumunci,kuma kana dagaskiya wajen ma gana(baka fadin qarya)kana girmama baaqo,kana taimakon gaskiya.
Haka akeso kema kikasance awajen mijinki,saisai yadunga alfahari dake .manzon Allah kobayan da Khajijah tarasu yana girmamawa tareda mutunta Qawayenta.
Ta rasu kafin hijira da shekara 3,har Aisha wata rana manzon Allah ya'ambaci Khadijah,sai dan kishinnan namata yamotsa tace tsowar kullum kake magana,ai Allah ya canza maka wa'yanda suka fita,sai yace Allah bai canzamin wanda suka fitaba domin itafa;
Tayi imani dani lokacinda mutane suka kafirce Mani,
Tayi mushaaraka dani cikin dukiyarta lokacin damutane suka hanani tasu dukiyar,
Kuma Allah ya azurtani da 'ya'ya da'ita,baibani watantaba,sai A'isha R.A tace gaskiya bazan sake magana akantaba (sabodata fahimci mat say in ta)
Manzon Allah idan yayanka akuya yana aikawa qawayen Khadija R.A,har wata rana akayi mashi magana akan hakan,sai yace ai ina son mai sonta shiyasa nake aika masu.
Allah yaqara mana son matan manzon Allah S.A.W(iyayen muminai)
0 comments:
Post a Comment