لقدجآءكم رسول من أنفسكم عزيز عليه ماعنتم حريص عليكم بالمؤمنين رءوف رحيم(٩:١٢٨)
Haqiqa wani irin manzo yazo muku daga cikinku,ai daga cikin jinsinku(mutunne kamar kowa tafannin halitta,ya mahaifi yanada mahaifiya,yanaci yana sha,sai Allah yafifitashi da wahayi da dabi'u nagartattu giye da kowa),duk abunda zai zama tsanani ga al'ummarsa yana damunsa matuqa,kuma mai tsananin kwadayin alkhairine gareku,kuma tabbas maitsananin tausayine da jinqai ga muminai(musulmai).
Shiyasa Allah Ta'aala ya bayyana abunda yake tabbatarda mutum yana son manzon Allah ko baya sons a,tahanyar cewa:
ومآءتاكم الرسول فخذوه ومانهاكم عنه فنتهواواتقوالله إن الله شديدالعقاب.
Na'ana;duk abunda manzon Allah yazo muku dashi to kuriqeshi,duk abunda yahaneku kuma kuhanu,kuji tsoron Allah cikin bin umurnin manzonsa,idan kuwa kukasaba masa to lallai Allah maitsananin uqubane.
وهذاشامل لأصولوالدين وفروعه وظاهره وباطنه،وأن ماجاء به الرسول يتعين على العباد،الأخذبه واتباعه،ولا تحل مخالفته.وأن نص الرسول على حكم الشيء كنص الله تعالى،لا رخصة لأحد ولاعذرله في تركه،ولا يجوزتقديم قول أحد على قو له صل الله عليه وسلم.
Wannan aya tagame asali na addinin musulunci da rasunansa,zahirinsa da badininsa(fili da boyen addini),duk abunda manzon Allah S.A.W yazo dashi dayashafi bayani akan ibaada wajine ayi riqo dashi akuma bishi,baya halatta asaa6a mass.Domin duk abunda manzon Allah yanassanta akan wani hukunci tofa kamar nassin Allah ne,saboda baya magana dason zuciya.
Don haka babu sauqi gawani daya daga cikin mutane ko uzuri agareshi yabar /yayi watsi da umurnin manzon Allah S.A.W.Kuma baya halatta(haramunne)agabaatar da maganar(umurnin)wani daya daga cikin mutane akan maganar manzon Allah S.A.W.
Hadeethi ya tabbata daga Abi Hurairah R.A cewa; manzo S.A.W yace:Idan na'umurceku dawani al'amari to kuzodashi(kuyishi)gwargwadon ikonku,kuma abundana haneku gameda aikatashi kunisanceshi.(Bukharin 7288)
أذاأمرتكم بأمروفأتوامنه ما استطعت مزز و ما نهيتكم عنه فاجتنبوه.
Shiyasa ko soyayya bakasamun masuson Manzon Allah dagaske sunason Wanda bayason Allah da Manzonsa,kamar yadda Allah Ta'ala yafada acikin littafinsa sura ta 58 ayata 22
لاتجدقوما يؤمنون بالله واليوم الأخريوآدون من حآدالله ورسوله ولوكانواءبآءهم أوأبنآءهم أوإخوانهم أوعشيرتهم....
Ma'ana bakata6a samun wa'yansu mutane dadukayi imanida Allah kuma sukayi imani daranar qarshe,suna qaunar wanda bayason Allah bayason manzonsa,wannan mutumin kowa koda iyayensane,ko 'ya'yansa,ko 'yan uwansa ko danginsa......
Fadin ina son manzon Allah dabaki kadai bazai isa mutum yakasance masoyinsa da Allah yake nufiba har sai akinsa yayi dai-dai dakarantar warsa.Sai duk wata ibada dazakayi tayi dai-dai dayadda manzon Allah yace ayita/yyayita.
Saboda kyawun ibadarka Allah bazai kar6etaba matuqar babu kwaikwayon manzon Allah.Allah Ta'ala ya fada cewa idan kuka bishi tabbas kunshiryu.
Hakanan cikin suratu Al-Imran ayata 31 Allah yana qalubalantar Wanda sukace baruwansu dabin manzon Allah dacewa;
قل إن كنتم تحبون الله فاتبعوني يحببكم الله ويغفرلكم ذنوبكم والله غفور الرحيم(٣١).
قل أطيعوا الله والرسول،فإن تولوافإن الله لا يحب الكافرين(٣٢).
Allah yace: kafada musu ya kai manzon Allah indai har dagaske kuna son Allah to kubini(kubi manzon Allah)idan kuka bini sai Allah yasoku kuma idan yasoku zai gaafarta muku zunubanku.(31)
Daya ayar kuma Allah yace:Kafada musu subi Allah subi manzonsa,inkuwa suka juya baya sukaqi bin Allah da manzonsa ,to lallai Allah bayason mutane kafirai.
Don cikkiyar soyayyar manzon Allah itace biyayya gareshi cikin duk abunda yazo dashi,yakuma qyamaci duk abunda manzon Allah yaqyamata kuma yahana.koda ranka yana son abu matuqar manzon Allah yahanashi to zaman lafiyanka kaguji wannan abun,koda zaka 6ata damutane,idan kuwa yace ayi abu koranka bayaso sai haqurtar dazuciyarka kabi umurninsa domin hakanne tsira agareka duniya dalahira.
Allah yaqara azurtamu dabin shiriyar manzon Allah S.A.W,
Allah yatausaya mana yagafarta mana laifukanmu,
Allah yarufa mana asiri duniya dalahira
0 comments:
Post a Comment