Wednesday, February 20, 2019

BAZAIYIWU KOWA YASOKABA ,KAIDAI NEMI SOYAYYAR ALLAH

Idan har manzon Allah swallallahu alaihi wasallam shugaban dayafi kowa cikin halittun Allah Ta'ala:
Gaskiya,
Adalci,
Riqon amana,
Tausayi,
Hakuri,
Jarunta,
Dattako,
Son talakawa,
Iya mulki,
Iya magana,
Ilimi,
Tsoron Allah,
Son musulunci,
Son Allah dama wa'yansu nagartattun halaye ya jagoranci mutane amma ansamu fandararru dasuka bijire masa,wa'yansuma sukace azzalumine Subhaanallah!.
Toh inaga wanda bashiba,wanda arashin uwane akanyi  uwar daki.
  Aqa'idar musulunci soyayya bata hana abayyana kuskuren mutum,musamman shugaban al'umma.
 Idan ana maganar adalcin shugabanni na musulunci baza'a taba mantawada ko tsallake Khalifan musulunci na biyuba wato Umar R.A.Saboda takatsan tsan akan dukiyar al'umma Umar R.A,tayadda hatta fitilar gwamnati idan yagama aikin al'ummar dayake jagoranta kashewa yakeyi,saiya kunna tashi domin hidimarsa da iyalinsa.Saboda tausayin Umar R.A wata rana yayi nufin ba wani shugabanci,sai yayi katobara yace shi baitaba sumbatar yaransaba,sai Umar R.A yafasa bashi,yace wannan yanuna bakada tausayi dajin qai.
Lokaci bayan lokaci yana rubuta saqo zuwa gwamnoninsa yana mai gardadinsu akan akodayaushe suzama masuyin abunda yakamata,sukasance masu gaskiya,amana da adalci.Duk Wanda yasamu da zalunci dacin amana yana hukuntashi.Dabba idan tayi tuntu6e hankalin Umar R.A tashi yakeyi,saboda tsoron kar Allah yatambayeshi meyasa baigyara hanyaba har dabba ke tuntu6e.
 Allahu Akbar!! mutane nawa ke mutuwa akan hanyoyinmu saboda rashin kyawun hanya?mutane nawa suke mutuwa adalilin yunwa?mutane nawa ke mutuwa akan rashin kudin magani wanda basutaka karaba ballanta sukarya.
Amma dukda haka Umar R.A idan yana kewayawa don sanin halin da talakawansa ke ciki yanajin qorafe qorafe kala-kala da tuhuma akan baya adalci.Amma duk lokacin dayaji haka ba fada yakeba zuwa yake yaji damuwarsu yayi masu maganinta.
Saboda haka duk wanda akaji yana qorafi idan akan wanda akesone,to kar ayanke masa hukunci akan qiyayyane,a'a tayuwu duk alkhairin da'ake samu shi baije ma saba,tayiwu soyayyar dayakeyima shugaba tasa bayajin dadin yaga anshiga haqqin wani,yanajima wannan masoyinnashi nauyin dayake akansa.
 Mutum nawa kasani suna sa6awa Allah?
Mutum nawa kasani suna sa6awa umurnin Allah?,
Amma bakanuna rashin jin dadinkaba sai sai soki wanda kakeso wanda idan akabi qeqeda qeqe kafishi matsayi awajen Allah.
Akoda yaushe addu'ar alkhairi,da addu'ar shiriya sune suka kamata bakunanmu suna furtawa,amma addu'ar halaka,lalacewa basune alkhairiba koda kuwa abunda mutum yakeyi yayi muni,to farko kayi masa addu'ar shiriya,idan cutarwarsa ga al'umma ya tsananta sai ka roqi Allah yayi maganinsa tayadda shi yaso batayadda kai kakesoba.Kamar yadda Abdullahi Dan Umar R.A yabamu labarin wani hadeethi:
عن عبد الله ابن عمر-رضي الله عنهما:أنه سمع رسول الله صل الله عليه وسلم يقول إذارفعرأسه من الركوع في الركعة الأخيرة من الفجر:اللهم العن فلاناوفلانا،بعدما يقول:سمع الله لمن حمده،ربنا ولك الحمد.
وفي رواية:يدعوعلى صفوان بن أمية،وسهيل بن عمرو،و الحارث بن هشام.
فأنزل الله:ليس لك من الأمرشىءأويتوب عليهم أويعذبهم فإنهم ظالمون(ال عمران:١٢٨).
Abdullahi Dan Umar R.A,wata rana yaji manzon Allah swallallahu alaihi wasallam yana cewa bayan ya dago kansa daga ruku'i acikin araka'ar qarshe na sallar asubahi:Allah yatsinema waane,da waane,bayan yace sami'Allahu liman hamidahu,Rabbana walakal hamdu.Acin wata ruwayar yana la'antar Swafwan ibn Umayyah,da Suhailu ibn Amru,da AlHarith ibn Hishaam.
Sai Allah yasaukar da wannan aya,Al'amarinsu ba ahunnunka yakeba,ko Allah yayafe masu/yakarbi tubarsu,ko kuma yayi masu azaba,tabbas su sunyi zalunci.Ay al'amarin Allah ne kadai zai yanke masu hukunci.Kaga su 'yannanfa suna cikin shugabannin mushrikai ayaqin Uhud,Kuma manzon Allah suka yaqa harsuka karya masa haqori,yakuma la'antarsu sai Allah yadakatar dashi.Kuma sai gashi Sun musulunta.
Don Allah duk wanda akaga ya karkace to abundayafi ataimaka masa da addu'ar shiriya,idan kuma cutarwarsa tayi yawa sai aroqi Allah yayi maganinshi tahanyar dayaga dama.Allah yaqara fahimtar damu,yagafarta mana laifukanmu,yasa mugama daduniya lafiya.

0 comments:

Post a Comment