Saturday, February 2, 2019

MAATA KUKIYAYE AMANAR ALLAH!!!!

قال الله تعالى:وقرن في بيوتكم ولا تبرجن تبرج الجاهلية الأولى،
الأحزاب٣٣
Allah Ta'ala yaa fara:kutabbata acikin gidajenku na karkuyi fitar tabarruji irin tabarrujin jahiliyyar farko.Ahzaab 33.
قال ابن كثير رحمه الله في تفسير هذه الآية:
أي؛ألزمن بيوتكم فلا تخرجن لغير حاجة،ومن الحوائج الشرعية.
Ibn Katheer ya fada acikin tafseerinsa acikin ma'anar wanna ayar:
Ay;kulazimci gidaajenku karku fita ba tareda wata buqaataba ta dole,dakuma buqaatu irinna shari'ar islaama.
تعريف التبرج :هو أن تظهر المرأة للرجل الأجانب الذين ليسوا من محارمها ما يوجب عليها الشرع أن تستر من زينتهاومحاسنها.
Ma'anar tabarruj:shine mace tabayyana abunda shari'a ta wajabta/shar'ant suturcewa/rufewa na kwalliyarta da kyayun jikinta ga ajnabi wanda ba muharramintaba.
التبرج للمرأة لها ثلاث معاني:
١-أن تبدي للأجانب جمال وجهها ومفاتن جسدها.
٢-أن تبدي لهم محاسن ملابسها وخليها.
٣-أن تبدي لهم نفسها بمشيتها وعملي له انت بناتها.
Tabarruji ga mace yana daukar ma'ana uku(3)
1-shine mace tabayyana kyawun fuskarta da bangaren dayake daukar hankalin maza ajikinta(yake fitinar da maza)ga ajnabinta(wandaba muharramintaba.
2-Mace tabayyana musu(maza)kyawawan tufafin data sanya ajikinta da kayan adonta(sarqa,'yan kunne,zobe da makamantansu)
3-Mace tabayyana musu(mazan)kanta tahanyar tafiyarta da rangwada da kuma sanya turare mai qamshi.
Yaa ke 'yar uwa mumina,kidaure kikatange kanki daga halaka tahanyar zama acikin gida,idan kuwa fita ta kaamaki to kifita cikin shiga irin ta shari'a
   Kuma arage yawan magana da mazanda daba muharramaiba domin shi ma ana lissafashi acikin tabarruji.
Saboda duk lokacin da'aka kika yawaita magana da namijindaba muharraminkiba shaquwace zata biyo baya.Idan maganar aurene wannan babu laifi haka akaso,amma idan kina da aure to kinga anshiga cikin sabon Allah.
Allah yaqara tsare mana imaninmu,yakuma gaafartaa mana zunubanmu baadan halinmuba.

0 comments:

Post a Comment