Wednesday, May 8, 2019

ALAQAR MUSULMI DA RAMADANA

Ko shakka babu yakamata aga canji arayuwar musulmi acikin ramadana.
Shidai watan Ramadan watane mai falalar gaske domin lokacine da Allah yake yima bayinsa rahma,gafara tareda 'yantasu daga wuta zuwa aljannah.Anaso musulmi lokacin ramadana yakasance mai:
Hakuri
Tausayi
Karamci
Yafiya
Kyauta
Yawan ibada
Karatun alqur'ani
Kame harshensa daga Qarya
Rintse ganinsa
Kiyaye jinsa
Kyautatama iyaye
kyautatama Moqota
kyautatama abokansa
Rufama dan uwansa asiri
Girmama Dan uwansa musulmi
Mai amfanar da jama'a
Sai mutambayi kanmu haka muke?
Saboda mu'amalarmu dayawa tananuna rashin tasirantawa da ramadana,mun dauka azumi shine kawai barin ci dasha da jima'i.
*sai kaga mutum yana azumi amma qarya itace sana'arsa,bayan manzon Allah S.A.W acikin hadithi ingantacce yace:duk wanda bai bar fadar qarya da aiki da itaba to fa Allah bashida buqatar barin cinsa da shansa.
*sai kaga bamu tausayama junanmu,musammam 'yan kasuwanmu sun maida lokacin Ramadan lokaci mafi tsadan kayan masarufi tareda cewa ba kayan bane ke qara tsada.
Sau dayawa saikaga anboya kayan dan asayar da tsada,har qanqara ta ruwa sai kaga ana sayenta Naira 40 #50.
To lallai ya kamata musani manzon Allah S.A.W yayi magana akan matsayin tausayi da kuma sauqaqawa  ga al'umma.
عن عائشة رضي الله عنها قالت:قال رسول الله صل الله عليه وسلم:إن الله رفيق يحب الرفق فى الأمر كله.
Daga Aisha R.A tace:Manzon Allah S.A.W ya ce: Lallai Allah mai tausayine yana son tausayi cikin al'amura gaba daya.Bukhari da Muslim suka fitar da hadithin.
و قال أنس رضي الله عنه،عن النبي صل الله عليه وسلم قال:يسرو ولا تعسرو،وبشرو ولا تنفروا.
Anas R.A yace manzon Allah S.A.W yace kusauqaqa karku tsananta ,kuma kuyi mutane bushara da abu maikyau karku koresu.
وقال صل الله عليه وسلم من يحرم الرفق يحرم الخير كله.رواه مسلم.
Hakanan manzon Allah S.A.W yace duk wanda bashida tausayi ya rasa alkhairi gaba daya.
To mike tunaninmu a irin rayuwar damuke ciki yanzu.Sai kaga wa'yanda ba muba sunfimu son junansu datausayin junansu.amma sai kaga musulmi baya son musulmi Dan uwansa yasamu sauqin rayuwa,koda yanada dalilin dazai taimakeshi bazaiyiba idanma yaga wata hanya da musulmi Dan uwansa zaisamu sauqin rayuwa zai iya hanawa.
Rayuwar damusulmai sukeyi ta wahala da anatausayin juna da ba hakaba da ansamu sauqi,saboda duk wanda kake taredasu kasan Wanda kafi kuma kasan wanda yake buqatar taimako.
Yana daga cikin hikimar farlanta azumi don mawadaci ya dandani irin abunda talaka yakeji dalilin zama da yunwa.Sai wannan yasa masa tausayi dajinqan mai qaramin karfi dayake qasa dashi.
Allah yatausaya mana yakarba mana azuminmu dasauran ibadunmu.Allah yasa mana tausayi dajinqan juna acikin zukatanmu.


0 comments:

Post a Comment