Ko shakka babu sallah tanada matsayi da muhimmanci maigirman gaske awajen musulmi,yana daga muhimmancinta:
*Sallah tana daya daga cikin rukunan musulunci,kuma tana matsayi na biyu daga shahadatain(Shaidawa babu abun bauta dagaskiya sai Allah,da shaidawa lallai annabi Muhammad manzon Allah ne)kuma itace rukuni mafi girma bayan shahada.
*Kuma sallah itace ginshiqin addinin musulmi,kamar yadda manzon Allah S.A.W yafada acikin hadithi sahihi,wanda Imam Attirmizi yafjtar dashi
قال رسول الله صل الله عليه وسلم:رأس الأمر الإسلام،وعموده الصلاة،وذروةسنامه الجهاد.
Manzon Allah S.A.W ya ce:kai na al'amari shine musulunci,kuma ginshiqinsa shine sallah,tsororuwarsa (qarshensa)jihadi.
Wannan hadithi nafiyayyen halitta S.A.W cike yakeda hikima domin kamar gidane/daki ,idan babu bango to baza'a iya rufe gidanba har azauna ciki,ko kuma gini idan aka cire ginshikinshi to saman zai fado.hakanan itama sallah idan musulmi bayayi to musuluncinsa zai fado(zai lalace)
*Sallah ita kadaice atsakanin sauran rukunan musulunci bayan shahadatain(Kalmar shahada),idan mutum yabarta yana kafirta,kuma kafirci dayake fitarda mutum daga musulunci.Matsaya biyu akan wanda yabar sallah:
1.Mutum yabar yin sallah,saboda kasala,ko kuma tozarta sallar tahanyar yinta lokacin da'akaga dama,ko yinta batare da kushu'i,ko natsuwa ba.Amma yana mai tabbatarwa azuciyarshi cewa wajibice wallah,to wannan za'ayi masa nasiha akirashi zuwa yatsaida sallah,yadunga yinta cikin jama'a.idan ya gyara to wannan haka akeso,idan kuma yacigaba akan halin dayake na wulaqanta sallah,to anan malamai sunyi sa6ani,akwai wanda sukace ya kafirta kuma idan ana shari'ar musulunci za'a kasheshi,bakuma za'ayi masa sallahba,sunkafa dalili da fadar Allah Ta'ala:
فإن تبوا وأقاموا الصلاة وأتوا الزكوة فإخوانكم في الدين
Allah yana magana akan mushrikai,idan suka tuba daga kafircin dasukeyi,suka tsayarda sallah,suka bayarda zakka,to sunzama 'yan uwanku acikin addini..
Malamai sukace acikin wannan aya ansa sharadi 3,amma duk al'amarin gudane,sharudan sune kamar haka:
-tuba daga shirka/kafirci/laifin
-tsayarda sallah
-bayarda zakka
Dole sai duka sharudan suncika mutum zaikace Dan uwa acikin musulunci.malamai sunce idan aka Sa sharadi guda days(1) ko sama da (1) akan wani abu,to abunda yake wajibi shine aciki sharudan duka ,idan daya baicikaba to kenan mutum bai cika sharadin da'aka ajiyeba.
2.Idan mutum yabar sallah yana mai inkarin wajabcinta(baiyarda cewa sallah wajibi bace),to wannan kafircine babu shakka,saboda qinyarda da wajabcin sallah ta farilla,kafircine tahanyar qaryata Allah da manzonsa,dakuma muminai.kamar yadda Allah yafada acikin suratul Nisa'i a ya ta 115:
ومن يشاقق الرسول من بعد كاتبين له الهدى ويتبع غير سبيل المؤمنين نوله ماتولى ونصره جهنم وسآءت مصيرا
Duk wanda yasa6awa manzon Allah S.A.W bayan shiriya tazo masa(anyi masa bayani), kuma yabi hanyar da bata muminaiba,Allah yace zamu ji6inta masa abunda yaji6inta kuma musashi cikin jahannama,Allah yace mokomata munana idan takasance jahannama.
Hakanan manzon Allah S.A.W yace lallai abunda yake tsakanin mutum da shirka da karfici,barin sallah.
Insha Allah zancigaba arubutu nagaba.Allah yabamu dacewa,yagafarta mana.
0 comments:
Post a Comment