Duk cikin aikin imani taimako da dukiya yafi wahala,amma wajen masu imani sunajin sauqin taimakawa da dukiyarsu ahanyar Allah.Wanda yana daga cikin ciyarwa/taimako acikin hanyar Allah taimakama Dan uwanka musulmi wanda kasan cewa yanada buqata ko baitambayeka ba,ballantana kuma idan har ya tambayeka akan kataimaka masa.
Shaidan kuma kullum bayason yaga mumini yana taimako domin yana daga cikin abun dayake kusantar da musulmi wajen Allah shigarda farin ciki azukatan halittun Allah musamman musulmi,idan Har za'ataimaki KARE asamu aljannar Allah ina ga wanda aikinshi kenan taimakawa Dan uwanshi musulmi akan wata buqata dayake da ita/damuwa?
Kaduba kaga yadda magbata suke aiwatar da imani azahiri;
جاء في تاريخ بغداد؛أن فقيراجاء إلى عبد الله بن المبارك،فسأله أن يقضي عنه دينا عليه سبعمائة درهم.فناوله عبد الله كتابا إلى وكيل ماله فذهب به الفقير،فلماقرأه الوكيل قال للفقير:كم الدين الذي سألت فيه عبد الله أن يقضيه عنك؟قال:سبعمائة درهم،فكتب الوكيل إلى عبد الله أن الرجل سألك أن تقضي عنه سبعمائة درهم،وكتبت له سبعةآلاف درهم،وسوف تغنى الأموال.فكتب إليه عبد الله:إن كانت الأموال قدفنيت غإن العمرأيضاقد فنى،فأجز له ماسبق به قلمي.
Ya zo acikin tarihin Baghdad,wani faqiri (matalauci) yaje wajen Abdullahi Dan Mubarak ,ya roqeshi yataimaka ya biya masa bashin da'ake binsa Dirhami dari bakwai(Dirhami 700)sai Abdullahi Dan Mubarak yarubuta takarda yabashi yakaima maikular masa da dukiya.sai wannan faqiri yatafi dawannan wasiqa(takarda) yakaimasa, Damaikula da dukiyar yakaranta sai yatambayi Faqiri nawane bashinda kanema yabiya maka? Sai yace Dirhami 700,sai mai kula da dukiyarnan ya sake rubutawa Abdullahi Dan Mubarak cewa shifa mutuminnan bashin Dirhami 700 yaroqi kabiya masa,kaikuma ka rubuta Dirhami 7000,ai dukiyar tana iya qarewa idan kabashi dirhami 7000.
Sai Abdullahi yasake rubuto ma maikula dakukiyarsa idan dukiya zata qare ai rayuwama tana qarewa,Kawai kabashi abunda narubuta.
Dirhami 1 dai-dai yake da Naira 98.60,kenan faqirinnan Naira dubu sittin da Tara da naira ishirin(N69,020)ya roqi yabiya masa ,amma yabashi Dirham Dubu bakwai akudin Nigeria N690,200,haka yabashisu saboda Allah batareda ya qasqantar dashiba.
Haka akeso duk lokacin da Dan uwanka musulmi yanemi kataimaka masa to kayi kokari kabashi taimakon da bayan yamagance damuwarsa zai samu abunda zai yi amfani dashi wajen sana'ar da zata taimaka masa da iyalinsa.Wannafa itace 'yan uwantaka amusulunci.Duk lokacin da Allah yahadaka da mutane suka nemi taimakonka sai kaqi taimakonsu kuma kana da iko,to sai Allah yatambayeka,Karka biyema shaidan cewa ai wahala kayi kasamu,shi wannan dayazo neman taimako wajenka daza'abashi zabin yayi irin wahalar dakayi da zaiyi,wahalarka dan uwa ba itace ta azurtakaba ,Wallahi Allah ne ,don akwai masu irin abunda kakeyi/kayi amma basu samu abunda kasamuba.Anan duniyane kadai kakeda damar dazaka taimaki Dan uwanka.
Amma saikaga mutum Allah yarufa masa asiri,saiya dunga gudun yan uwa da abokansa,ko zuwa wajensu saikaga bayayi saboda yana ganin su basu isa yaje yaziyarcesuba.
Wani bawan Allah yake mani korafi wata rana cewa shi wallahi yana qoqarin zuwa wajen 'yan uwansa zumunci,wani lokacinma yaje ace wai bacci sukeyi,shikuma ko hidimar gidanshi basu zuwa idanba mutuwa akayiba,ballantana kuma suzo masa ziyara haka kawai,sai yake ce Mani shi wallahi kamar yabar zuwa.Sai nace a'a kai kacigaba da zumuncin dakakeyi,ai Allah yasan zuciyarka,nakuma ce masa al'ummace yanzu idan bakada wani abu ahunnunka ba kowa ke kulakaba ballantana yazo inda kake,haka mafi yawa ake.
Allah yasanya mana tausayi acikin zukatanmu,yasa mana ganin darajar yan uwanmu musulmai da abokanenmu acikin zukatanmu.Allah karka ba shaidan dama yasamu galaba akanmu
0 comments:
Post a Comment