Thursday, January 31, 2019

ALLAH KADAI AKE ROQO

A 'aqeeda ta musulunci da aka aiko manzon Allah S.A.W dashi,Allah kadai ake roqo.Akwai dayawa daga cikin masu kiran Kansu musulmai ,amma suna roqon wani wanda ba Allah ba,daga cikin annabawa,mala'iku,waliyai(masu rai dama wanda suka mutu) sai kaji ana kiran waniwani wanda ba Allah akan yabiya wata buqata wanda Allah kadai yakebanta dawannan aikin,kamar roqon;
Haihuwa,
Arziqi,
Ilimi,
Lafiya,
Matsayi,
Aljannah,
Yaye damuwa,
Kawo kasuwa,
Agajin da Allah kadai ke iyawa.
Lallai duk mai roqon wani wanda ba Allah ba daya daga cikin wa'yannan ko dukaduka,to tabbas yana cikin masu shirka,dalilin fadar Allah Ta'ala:
Kada kuroqi wanda ba Allah ba,wanda bazai iya amfanarkaba kuma bazai iya cutar dakaiba,Idan kuwa harka aikata haka(karoqi wanin Allah),to tabbas kana cikin azzalumai(mushrikai-kafirai) "Yunus ayata 106".
 Kuma manzon Allah S.A.W have: addu'a ibadace(bautace).kamar sallah ce,baya halatta ayima wani Sallah danufin yabada sakamakonta idan ba Allah ba,koda kuwa manzon Allah be.
   Sai dai;akwai taimako na dabi'a wanda abokin halitta dan uwanka zai iya yimaka,wannan basu ake nufiba.
Allah yadatar damu,yajiqanmu,yagafartaa mana laifukanmu yakuma kame hannayenmu yahanamu saba masa.Ameen

0 comments:

Post a Comment