• This is Slide 1 Title

    This is slide 1 description. Go to Edit HTML and replace these sentences with your own words.

  • This is Slide 2 Title

    This is slide 2 description. Go to Edit HTML and replace these sentences with your own words.

  • This is Slide 3 Title

    This is slide 3 description. Go to Edit HTML and replace these sentences with your own words.

Wednesday, May 8, 2019

ALAQAR MUSULMI DA RAMADANA

Ko shakka babu yakamata aga canji arayuwar musulmi acikin ramadana.
Shidai watan Ramadan watane mai falalar gaske domin lokacine da Allah yake yima bayinsa rahma,gafara tareda 'yantasu daga wuta zuwa aljannah.Anaso musulmi lokacin ramadana yakasance mai:
Hakuri
Tausayi
Karamci
Yafiya
Kyauta
Yawan ibada
Karatun alqur'ani
Kame harshensa daga Qarya
Rintse ganinsa
Kiyaye jinsa
Kyautatama iyaye
kyautatama Moqota
kyautatama abokansa
Rufama dan uwansa asiri
Girmama Dan uwansa musulmi
Mai amfanar da jama'a
Sai mutambayi kanmu haka muke?
Saboda mu'amalarmu dayawa tananuna rashin tasirantawa da ramadana,mun dauka azumi shine kawai barin ci dasha da jima'i.
*sai kaga mutum yana azumi amma qarya itace sana'arsa,bayan manzon Allah S.A.W acikin hadithi ingantacce yace:duk wanda bai bar fadar qarya da aiki da itaba to fa Allah bashida buqatar barin cinsa da shansa.
*sai kaga bamu tausayama junanmu,musammam 'yan kasuwanmu sun maida lokacin Ramadan lokaci mafi tsadan kayan masarufi tareda cewa ba kayan bane ke qara tsada.
Sau dayawa saikaga anboya kayan dan asayar da tsada,har qanqara ta ruwa sai kaga ana sayenta Naira 40 #50.
To lallai ya kamata musani manzon Allah S.A.W yayi magana akan matsayin tausayi da kuma sauqaqawa  ga al'umma.
عن عائشة رضي الله عنها قالت:قال رسول الله صل الله عليه وسلم:إن الله رفيق يحب الرفق فى الأمر كله.
Daga Aisha R.A tace:Manzon Allah S.A.W ya ce: Lallai Allah mai tausayine yana son tausayi cikin al'amura gaba daya.Bukhari da Muslim suka fitar da hadithin.
و قال أنس رضي الله عنه،عن النبي صل الله عليه وسلم قال:يسرو ولا تعسرو،وبشرو ولا تنفروا.
Anas R.A yace manzon Allah S.A.W yace kusauqaqa karku tsananta ,kuma kuyi mutane bushara da abu maikyau karku koresu.
وقال صل الله عليه وسلم من يحرم الرفق يحرم الخير كله.رواه مسلم.
Hakanan manzon Allah S.A.W yace duk wanda bashida tausayi ya rasa alkhairi gaba daya.
To mike tunaninmu a irin rayuwar damuke ciki yanzu.Sai kaga wa'yanda ba muba sunfimu son junansu datausayin junansu.amma sai kaga musulmi baya son musulmi Dan uwansa yasamu sauqin rayuwa,koda yanada dalilin dazai taimakeshi bazaiyiba idanma yaga wata hanya da musulmi Dan uwansa zaisamu sauqin rayuwa zai iya hanawa.
Rayuwar damusulmai sukeyi ta wahala da anatausayin juna da ba hakaba da ansamu sauqi,saboda duk wanda kake taredasu kasan Wanda kafi kuma kasan wanda yake buqatar taimako.
Yana daga cikin hikimar farlanta azumi don mawadaci ya dandani irin abunda talaka yakeji dalilin zama da yunwa.Sai wannan yasa masa tausayi dajinqan mai qaramin karfi dayake qasa dashi.
Allah yatausaya mana yakarba mana azuminmu dasauran ibadunmu.Allah yasa mana tausayi dajinqan juna acikin zukatanmu.


Wednesday, May 1, 2019

ILLOLIN ZUWAN MATA WAJEN 'YAN TSIBBU/BOKAYE

Ana samun mata masu yawa da dabi'ar bin 'yan tsibbu da Bokaye saboda manufofi daban daban.
Amma mafi yawa abun dayake kai mata wajen bokaye dalilaine kamar haka:
*jayayyada umurnin Allah
*fada da qaddarar Allah
*sa6ama umurnin manzon Allah
*rashin imani
*rashin tausayi
*hassada
*rashin tawakkali 
Mafi yawan sihirin da mata sukafiyi shine
السحر التفريق:للتفريق بين:
الرجل وأمه
الرجل و أبيه
الرجل وأخيه
الرجل وصديقه
الرجل وشريكه في التجارة
أو التفريق بين الرجل وزوجته،و هذا النوع أخطرها و أكثرها انتشارا
Sihiruttafriq anayin sane don raba:
-Tsakanin mutum da mahaifiyarsa
-Mutum da mahaifinsa
-Mutum da Dan uwansa najini
-Mutum da abokinsa
-Mutum da abokin kasuwancinsa
-Kuma anayi dan raba tsakanin mutum da matarsa,kuma wannan au'in shiyafi hatsari kuma shiyafi yaduwa/shi mata sukafi yawanyi
Babban dalilin mata na fadawa cikin wannan halakar shine KISHI.
Akasarin mata akan kishiya suke halaka.
Wani lokacin uwargidance zakasamu dawannan matsalar,wani lokacin kuma wadda aka auro daga baya itaceke lalata gida.
Mutum yana zauneda matarsa lafiya lokaci daya saikaga yatsaneta,ko sunanta bayaso yaji an ambata,kuma daza'a tambayeshi dalilin dayasa baya sonta shikanshi baisaniba.Duk wace mai wannan mummunar dabi'ar tana  jefa kanta cikin bala'i kala-kala,daga ciki:
*Manzon Allah yace baya tareda ita;
من جنب على امرئ زوجته فليس منا.
أخرجه أبوداود
Manzon Allah S.A.W yace duk wanda yanisanta/yaraba mutum da matarsa to bataya tare damu.
*Allah tana fushi da'ita.
*ba'a karbar sallarta.
*Allah yatsinemata domin ta raba zumunci
*Tanasa mijinta yaqiyin adalci atsakanin matansa,Wanda hakan matsalane agareshi da'ita,
*tana shiga cikin masu annamimanci dukda sihirin datakeyi bai isheta kullum tana yawon hada wannan matarda mijinta,mutanenda taga suna shiri da'ita,yara da babansu wa'yanda ba 'ya'yantaba,
*tana shiga cikin masuyin giba,
*mafi yawa zaka'iske fasiqace saboda mafiyawan 'yan tsibbu da bokayen datakebi sai sunyi lalata da'ita sannan sukeyi mata aikin da take so,
*kodayaushe tana fama da ciwon zuciya saboda ciwon hassada.
*batajin kunyar zagin mutum amma agaban idonsa akasin haka.
*batajin kunyar yin qarya
*koda yaushe baka rabata da laya,ajikin skirt din ta,hannun zanenta,jikin pant din ta,cikin pillow na Maigida dasauran gurare
*komin dadewa wata rana saita baki tausayi saboda duk tsawon lokacinda akadauka tana cutama mijin da matansa lokaci daya abun zai lalace.
*duk gidahen bokaye da 'yan tsibbun datake zuwa batareda izinin maigidanta take zuwaba,mala'iku na tsine mata.
Allah ya shiryi masu wannan muguwar halayyar.

Saturday, April 20, 2019

LETS PUT OUR HANDS TOGETHER AND SAY NO TO OPEN DEFECATION

Open defecation is the human practice of defecating outside (in the open environment) rather than into a toilet. People may choose fields, bushes, forests, ditches, streets, canals or other open space for defecation. They do so because either they do not have a toilet.The practice is common where wastes disposal infrastructure and services are not available. Even if toilets are available, efforts may still be needed to promote the use of toilets.
About 892 million people, or 12 percent of the global population, practiced open defecation in 2016.Seventy-six percent (678 million) of the 892 million people practicing open defecation in the world live in just seven countries.
Open defecation can pollute the environment and cause health problems,like :
-cholera,
-dysentary
-dirrhoea
-Polio
-hepatitis A
-typhoid
-Schistosomiasis/bilharzia
-trachoma
-malnutrition
-intestinal worm
High levels of open defecation are key to
*high child mortality,
*poor nutrition,
* poverty, and
* large disparities between rich and poor.
Actually,I believed that the solution to open defecation requires the involvement of individuals,house holds and government.The government should do the best it can in the provision of adequate toilets and water,there is also a need for education and awareness to correct some negative norms and beliefs of the people.
Its happen to be a common thing to find human faeces around the public areas,even in the cities across the country,as such there is need for a strong penalty on any body fought defecating in an open spaces.
Unarguably,adequate sanitation with good hygiene and safe /clean water are fundamental to good health, social and even economical development.
 Note:to my awareness there no religion in the world that teaches poeaple to pollute their environment,like in Islam its forbidden to defecate by the road,canals(water bodies),or in pubic.
Say no to this inhuman practice.


Wednesday, April 17, 2019

مفاتيح النار للنساء(MABUDAN WUTA GA MATA)

Ya ke 'yar uwa na tabbata
ke musulmace kuma kinyarda da manzon Allah S.A.W,kuma kitabbata cewa duk abunda yafada gaskiyane,to hakika Hadithi ya tabbata daga manzon Allah S.A.W:
Abdullahi Dan Abbas R.A yace:Manzon Allah S.A.W yace :annuna mani aljannah sainaga mafi yawan 'yan cikinta talakawane,kuma annuna mani wuta sainaga mafiya yawan 'yan cikinta Matane.
Haka ma Abi Hurairah da Abdullahi Dan Umar R.A sunfadi irin abunda Dan Abbas yafada suma sunjine daga bakin manzon tsira S.A.W.
 *Ko kinsani 'yar uwa daga cikin abunda yake kai mata wuta akwai;SIHIRI
السحر من مفاتيح النار للنساء،سواء كان القيام بعمل السحر أو الذهاب إلى الساحر وتصديقه.
Sihiri yana daga cikin mabudin shiga wuta ga mata,kodai takasance ita keyinsa da kanta kokuma zuwa takeyi anayi mata to duk dayane.
 Manzon Allah S.A.W yace :duk Wanda yaje yaje wajen mai sihiri yakuma yarda da abunda yafada masa,to ya kafircewa abunda aka saukarwa Muhammad S.A.W.,Dan haka babu makawa maiyin sihiri ko wanda yake zuwa ayi masa yana kafirta.
Shikuwa idan mutum yamutu kafiri babushi babu shiga aljannah.
 Sau dayawa Mata idonsu yana rufewa akan al'amarin kishiya(abokiyar zamanta)saikaga tashiga bin malaman tsibbu(bokaye)duk wani lungu dasaqo idan taji labarin irin wa'yannan batattun saitaje,saboda buqatunta,kadan daga cikin abundance take buqata ayimata sune:
*Zata buqaci asawa mijin qin abokiyar zamanta,
*Zata buqaci amaido hankalinshi kanta kadai,
*yakasance maganarta kawai yake saurare,
*Komin muhimmacin abu idan ba ita tace ayiba to bazaiyiba,
*Tana raba zumuncin miji da 'yan uwansa,
*Tanasa miji yatsani 'yayan daba nataba,
*Dukiyarsa gaba daya tana komawa karkashin ikonta
*Tana fitarda abokiyar zamanta daga cikin gidan.
 wannan kadan kenan daga cikin mugun aikin mata masu bin malaman tsibbu.
Tabbas kyautatawar mace ga mijinta yanasa mijin yaso matar,amma ba irin son dayawuce dabi'a ba.
Saboda sona Allah baya sanya mutum ya dinga bin umurnin matarsa harya sa6awa Allah.Sona Allah bayasa miji yabi ra'ayin matarsa wajen yanke zumunci tsakaninsa da 'yan uwansa,amma agefe daya kuma saikaga shi mijin yana rawar jiki wajen kyautatawa danginta.
Kuma duk laifin daxatayi bazai ta6a ganinsa amatsayin laifiba.
Shiyasa Manzon Allah S.A.W yace
عن ابن مسعود رضي الله عنه قال:سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:إن الرقى والتمائم والتولةشرك
Daga Dan Mas'ud R.A.yace naji manzon Allah S.A.W yana cewa:Lallai Ruqya wadda bata shari'a ba,da daura/rataya laya,guru ko kambu,da sihirinda akeyi domin mallake miji,rabashi da matarsa(bita zaizai)Dukkansu shirkane.
Qarin bayani akan wannan hadithin zaizo arubutu nagaba insha Allahu.sannan kuma zamuga illoli da hatsarin da mace ke fadawa adalilin bin 'yan tsibbu,yaya qarshenta yake kasancewa.Allah yatsare mana 'yan uwanmu mata harma da mazan daga bin wannan mummunan hanya.

Thursday, March 21, 2019

TAIMAKAMA DAN UWANKA MUSULMI DON ALLAH,ALAMANE NA IMANI

Duk cikin aikin imani taimako da dukiya yafi wahala,amma wajen masu imani sunajin sauqin taimakawa da dukiyarsu ahanyar Allah.Wanda yana daga cikin ciyarwa/taimako acikin hanyar Allah taimakama Dan uwanka musulmi wanda kasan cewa yanada buqata ko baitambayeka ba,ballantana kuma idan har ya tambayeka akan kataimaka masa.
Shaidan kuma kullum bayason yaga mumini yana taimako domin yana daga cikin abun dayake kusantar da musulmi wajen Allah shigarda farin ciki azukatan halittun Allah musamman musulmi,idan Har za'ataimaki KARE asamu aljannar Allah ina ga wanda aikinshi kenan taimakawa Dan uwanshi musulmi akan wata buqata dayake da ita/damuwa?
 Kaduba kaga yadda magbata suke aiwatar da imani azahiri;
جاء في تاريخ بغداد؛أن فقيراجاء إلى عبد الله بن المبارك،فسأله أن يقضي عنه دينا عليه سبعمائة درهم.فناوله عبد الله كتابا إلى وكيل ماله فذهب به الفقير،فلماقرأه الوكيل قال للفقير:كم الدين الذي سألت فيه عبد الله أن يقضيه عنك؟قال:سبعمائة درهم،فكتب الوكيل إلى عبد الله أن الرجل سألك أن تقضي عنه سبعمائة درهم،وكتبت له سبعةآلاف درهم،وسوف تغنى الأموال.فكتب إليه عبد الله:إن كانت الأموال قدفنيت غإن العمرأيضاقد فنى،فأجز له ماسبق به قلمي.
Ya zo acikin tarihin Baghdad,wani faqiri (matalauci) yaje wajen Abdullahi Dan Mubarak ,ya roqeshi yataimaka ya biya masa bashin da'ake binsa Dirhami dari bakwai(Dirhami 700)sai Abdullahi Dan Mubarak yarubuta takarda yabashi yakaima maikular masa da dukiya.sai wannan faqiri yatafi dawannan wasiqa(takarda) yakaimasa, Damaikula da dukiyar yakaranta sai yatambayi Faqiri nawane  bashinda kanema yabiya maka? Sai yace Dirhami 700,sai mai kula da dukiyarnan ya sake rubutawa Abdullahi Dan Mubarak cewa shifa mutuminnan bashin  Dirhami 700 yaroqi kabiya masa,kaikuma ka rubuta Dirhami 7000,ai dukiyar tana iya qarewa idan kabashi dirhami 7000.
Sai Abdullahi yasake rubuto ma maikula dakukiyarsa idan dukiya zata qare ai rayuwama tana qarewa,Kawai kabashi abunda narubuta.
 Dirhami 1 dai-dai yake da Naira 98.60,kenan faqirinnan Naira dubu sittin da Tara da naira ishirin(N69,020)ya roqi yabiya masa ,amma yabashi Dirham Dubu bakwai akudin Nigeria N690,200,haka yabashisu saboda Allah batareda ya qasqantar dashiba.
Haka akeso duk lokacin da Dan uwanka musulmi yanemi kataimaka masa to kayi kokari kabashi taimakon da bayan yamagance damuwarsa zai samu abunda zai yi amfani dashi wajen sana'ar da zata taimaka masa da iyalinsa.Wannafa itace 'yan uwantaka amusulunci.Duk lokacin da Allah yahadaka da mutane suka nemi taimakonka sai kaqi taimakonsu kuma kana da iko,to sai Allah yatambayeka,Karka biyema shaidan cewa ai wahala kayi kasamu,shi wannan dayazo neman taimako wajenka daza'abashi zabin yayi irin wahalar dakayi da zaiyi,wahalarka dan uwa ba itace ta azurtakaba ,Wallahi Allah ne ,don akwai masu irin abunda kakeyi/kayi amma basu samu abunda kasamuba.Anan duniyane kadai kakeda damar dazaka taimaki Dan uwanka.
Amma saikaga mutum Allah yarufa masa asiri,saiya dunga gudun yan uwa da abokansa,ko zuwa wajensu saikaga bayayi saboda yana ganin su basu isa yaje yaziyarcesuba.
 Wani bawan Allah yake mani korafi wata rana cewa shi wallahi yana qoqarin zuwa wajen 'yan uwansa zumunci,wani lokacinma yaje ace wai bacci sukeyi,shikuma ko hidimar gidanshi basu zuwa idanba mutuwa akayiba,ballantana kuma suzo masa ziyara haka kawai,sai yake ce Mani shi wallahi kamar yabar zuwa.Sai nace a'a kai kacigaba da zumuncin dakakeyi,ai Allah yasan zuciyarka,nakuma ce masa al'ummace yanzu idan bakada wani abu ahunnunka ba kowa ke kulakaba ballantana yazo inda kake,haka mafi yawa ake.
Allah yasanya mana tausayi acikin zukatanmu,yasa mana ganin darajar yan uwanmu musulmai da abokanenmu acikin zukatanmu.Allah karka ba shaidan dama yasamu galaba akanmu

Friday, March 15, 2019

MANZON ALLAH (S.A.W)KADAI AKEBI IDO RUFE!!!

Wallahil Azeem!!:Allah bazai tambayekaba idan bakabi,malam waneba,ko shehi waneba sannan bazai kamaka dalaifiba idan baka shiga kungiyar Izala ko Dariqa ba.
Amma tabbas Allah zai tambayeka tareda azabtarwa maitsanani idan bakabi manzon daya'aiko makaba,Muhammad swallallahu Alaihi was all am.Sannan kuma Allah zai kaamaka dalaifi idan kaqibin Qungiyar Sahabban Manzon Allah Swallallahu alaihi was all am.
Saboda duk duniya babu wanda Allah ya'aiko maka,wanda kuma dole awajensa zaka koyi addini irin kuma kafahimceshi,kuma idan kayi aikin Allah yakar6a sai Annabin Allah kuma manzonsa Muhammad Swallallahu alaihi wasallam.
قال الله تعالى:هواالذي أرسل رسوله بالهدىودين 
لحق ليظهره على الدين كله وكفى بالله شهيدا(٢٨)
محمد الرسول الله،والذين معه أشدآء على الكفار رحماء بينهم.....(٢٩)
Allah Ta'ala yana fada acikin suratul Fathi ayata 28-29 cewa:Allwh shine wanda ya'aiko manzonsa Annabi Muhammad S.A.W dashiriya dakuma addinin gaskiya(musulunci)don yarinjayarshi akan duk wani addinin dabashiba kuma lallai Allah ya'isa yazama maisheda akan hakan.
 Muhammadu Manzon Allah ne(Allah yana shedawa duniya akan masu qaryata manzoncin annabi S.A.W ,ko sunqi ko sunso Allah ya tabbatar dakasancewarshi manzonsa,wanda yazo dasaqon addinin musulunci )wa'yanda suke taredashi(sahabbansa)basu jiyar dakafirai dadi,basu sassauta mash,amma suna jinqan junansu suna tausayin junansu(suna taimakama junansu,basuson abunda zai jefa 'yan uwansu cikin halin qaqanikayi.......
Duk duniya Manzon Allah kadaine yakamata yazama madubi awajenka ,duk bunqasar malami ana binshine idan abunda yake fada ko yake koya mana yayi dai-daida karantarwar manzon Allah S.A.W.
   Saboda shikadaine binsa yake addini sa6a masa kuma yake jawoma mutum fushin Allah,kamar yadda Allah yatabbatar manada haka,cikin suratu Noor ayata 63
فليحذر الذين يخالفون عن أمره أن نصيبهم فتنة أويصيبهم عذ اب أليم
Masu sa6a umurnin manzon Allah suji  tsoron fitina sakamakon sa6a masa,ko kuma wata azaba mai radadi.
قال الله تعالى:من يطع الرسول فقد أطاع الله و من تولى فما أرسلناك عليهم حفيظا
Duk wanda yayimaka biyayya to tabbas Allah yayimawa,.....
وقال تعالى:وما ءاتاكم الرسول فخذوه ومانهاكم عنه فانتهوا،والتقوا الله،إن الله شديد العقاب(الحشر:٧)
Duk abunda manzon Allah S.A
.W yakawo muku/ya umurceku tokuriqeshi dakyau,sannan duk abunda yahaneku akansa to kuhanu daga aikatashi,kuji tsoron Allah,lallai Allah mai tsananin uqubane akan masu sa6ama umurnin manzon Allah
Kaf duniyar nan babu Wanda akaba saqon addinin musulunci sai manzon Allah,kuma ya'isar dasaqon Allah.
Wallahi babu wani abu acikin addini da idan aka aikatashi za'asamu lada fache saida manzon Allah yayi bayaninsa.
ADDININ ALLAH YAGAMA CIKA TUNKAFIN MANZON ALLAH YABAR DUNIYA,ALLAH YATABBATAR DAHAKAN.
Kuma dole saikayi Ibada yadda manzon Allah S.A.W yayi sannan zaka samu ladar abunda kayi wajen Allah.
Muhadu arubutu nagaba;Ba malam,wane,ko shehi wane aka aiko makaba.
Allah yadatardamu dabin sunnar manzon Allah  S.A.W.


Tuesday, March 12, 2019

SUGABANCIN QASATA NIGERIA

 Kai talakan Nigeria wallahi yakamata kadawo hayyacinka,dangane da qoqarin ganin ka 6ata ma wani rai akan shuwagabannin da mafi yawa batakai sukeba.Ko addini kakeyi don ka6atama wani rai to bakada lada.Amma abun mamaki dayawa daga cikin talakawa idonmu ya rufe akan wani wanda wallahi idan za'a rasaka bazaiji ko ajikinsa ballantana yaji damuwa indai har rasaka zaisa yacimma manufarsa.
 Abun mamaki wani lokacin saikaga harda malamanmu,basu auna maganganun dasuke furtawa akan siyasa dakuma Dan siyasar Nigeria.Tayadda zakaga/zakaji malami yana fadin maganganunda mai ilimin addini kuma akan fahimtar magabata nakwarai baikamata yana yinsu.Bayan duk ta bayyana babu irin rashin gaskiyarda kiwane Dan jam'iyya bayayi hasalima mafiyawan wa'yanda ake tsarkakewa abunda yayisu shiyayi wa'yanda ake zagi.
Ni haryanzu abunda kasa yarda dashi shine duk cewa duk Dan jam'iyyar su wane duk lalacewarsa,duk rashin gaskiyarsa indai Dan jam'iyyajam'iyyar wanene/suwane mutumin banzane.Shikuwa wanda baya cikin jam'iyyar suwane koda ya fi Dan jam'iyyarsu wane nagarta.
Nidai abunda nasani wanda yake saman mulki yafi damar yin magudi sama da wanda yake bashida mulki.
Kuma indai gaskiya da adalci za'ayi mutum bazai dage ala dole saiya zarce kuma kotawane hanya.
Amma tabbas yakamata mudawo mufuskanci gaskiya,babu laifi kayautatama mutum zato kuma dunga yabonshi akan kyawawan halayensa,amma hakan bai bude kofar shiga gaban Allah da manzonsaba,wajen magana da aiki kamar yadda Allah Ta'ala yafada acikin littafinsa mai tsarki:
يأيها الذين أمنواولا تقدموابين يدي الله ورسوله واتقوا الله،إن الله سميع عليم(١).
Allah ya fada cewa:ya ku wa'yanda kukayi imani(kuka bada gasikiya da Allah),karku shiga gaban Allah damanzonsa akan wajen furta wani abu aikata wani aiki acikin addinin musulunci,kuji tsoron Allah lallai Allah mai jine akan duk abunda kuke furtawa kuma mai cikakken ilimi akan duk abunda bayinsa suke aikatawa afili da boye.
 Don haka lallai mudinga taka tsan-tsan akan tsarkake kawunanmu,Domin shi Allah shikadaine yasan abundake fili da 6oye,masanin abun dayake cikin zukatan bayinsa.Tabbas akwai nagartattu acikinmu amma abudake namu shine mukyautata masu zato,tahanyar cewa da'alama wane waliyin Allah ne,tahanyar la'akarida halayen waliyyai dayakedasu cikin irin siffofinda Allah ya fada ko manzonsa S.A.W.Amma sai kaji wani harmada rantsuwa cewa wane waliyyine.Maimakon yace Wallahi duk wanda yasiffantu da siffofin waliyyai da Allah yabayyana ko manzonsa ,Wallahi waliyyine.Allah ya fada awani bangaren ayata 32 cikin suratul Najmi
فلا تزكوا أنفسكم،هو أعلم بمن اتقى.
Allah yana cewa karku tsarkake kawunanku shi Allah shine mafi sanin maijin tsoransa.
 Kawai ayi gaskiya aba jama'a wanda suka za6a,tundadai ba wahayi akayiba akan dole sai dan jam'iyya kaza yaci za'a bada mulki,shikuma dan jam'iyyar adawa idan yaci sai ayi amfanida "inconclusive ".
 . Wai anmaida shugabanci business din dayafi tara/kawo kudi masu yawa.
INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'OUN!!!